Monday, 15 January 2018

Fasahar Zamani

TAKAITACCEN TARIHIN FACEBOOK 



Sunan Facebook ba boyayye bane ga matasan wannan zamani maza da mata, musamman masu mu’amala da fasahar ziyarar yanar gizo. Domin kuwa koda mutum baya amfani da shafin ba zai kasa jin masu mu’amala da shi suna zancensa ba. Duk da dai ba duk aka taru aka zama daya ba wato dai ba za’a rasa‘yan tsirarun mutanen da basu san wannan shafi na Facebook ba, ko kuma idan sun san shi basu san wace irin mu’amala ake dashi ba, kai wasu ma suna amfani da shafin amma basu fahimce shi ba, domin kuwa idan zaka tambaye su menene amfanin Facebook, ka basu aiki ba karami ba. To idan kana daya daga cikin wanda basu san menene Facebook ba ko kuma kana daya daga cikin wadanda sun sanshi amma basu san amfaninsa ba, kai har ma da wadanda suka san shafin kuma suka san amfaninsa ku dan bani hankalinku na dan lokaci dan sanin menene Facebook, wa ya kirkire shi, don me aka kirkire shi, menene amfaninsa da sauran batutuwa makamantan hakan. 


MENE NE FACEBOOK?

        Facebook dai dandali ne na sada zumunta kuma yana daya daga cikin miliyoyin shafukan dake kunshe a rumbun yanar gizo wato Internet. Wato kamar irinsu shafukan Twitter, MySpace, Google+ da sauransu, sai dai shafin na Facebook ya banbanta da shafukan dana bayyana a sama ta hanyoyi da dama. Facebook shafi ne da wani dalibi mai suna Mark Zuckerberg ya kirkire shi tare da wasu abokan karatunsa su uku Eduardo Saverin, Dustin Moskovitz da kuma Chris Hughes. A ranar 4 February 2004. A makarantar Harvard a jihar Califonia dake kasar Amurka. Wadannan dalibai sun kirkiri shafin ne don amfani dashi a makarantarsu kawai, don haka cikin dan lokaci kankani shafin ya baibaye ilahirin wannan makaranta, saboda irin farin jinin da shafin ya samu a wurin daliban makarantar Harvard ba’a dau lokacimai tsawo ba shafi ya tarwatsu zuwa sassan manyan makarantun kasar Amurka baki daya. Kafin kace me tuni shafin ya tsallaka zuwa kasashen Canada da England, wajen shekarar 2005 shafin ya karade gaba dayan yankin kasashen turawa da yankin Amurka ta kudu. A ranar 26 ga watan 9 na shekarar 2006 kamfanin Facebook ya bayyana cewar kowa zai iya mallakar shafina duk inda yake a duniya indai ya haura shekaru 13 da haihuwa. Shafin Facebook shafi ne da kowa zai iya amfani dashi cikin sassakar hanya, shafi ne da masu amfani dashi ke samun damar haduwa da mutane kala kala daga kasashen duniya daban – daban, shafin yana da kayatarwa, nishadantarwa, ilimintarwa, shagaltarwa har ma dawa’azantarwa. Shafi ne daya hada al’ummatai kala – kala mabanbanta ra’ayi, kabila, addini, yare da kuma tarbiya. Haka yasa duk irin manufar da tasa mutum amfani da shafin yake samun ‘yan uwansa. Facebook wani dandali ne daya bawa masu amfani dashi dama wurin baja kolen ra’ayinsu, ba tare da tsangwama ko hana ‘yancin magana ba, wannan dalilinsa Facebook ya tserewa dukkan wani shafi na sada zumunta wato social network a turance yawan masu amfani dashi. Kamar yadda kamfanin ya shaida cewar yana da sama da mutum miliyan 750 masu amfani da shafin a kiyashin da akayi a watan bakwai na shekara ta 2011. 

RABE-RABEN MASU YIN FACEBOOK 

Kamar yadda muka sani ne cewa facebook ya zama dandali na sada zumunta ga mutanen duniya gaba daya. Wanda ya hada masu matakin karatu kala daban-daban, sannan ya hada masu fahimta kala daban-daban, saboda haka muka fahimci cewa zaka iya kasa masu amfani da facebook gida 12. 
1. Mai kallo Wasu daga cikin masu yin amfani da facebook suna yi ne dan kallon hotunan wasu, posting da comment nasu. Su basa post, balle comment kuma basa Like idan sun ga rubutu ko hoto. Amma zasu baka labarin post ko Comment din da kayi matukar ya sanka zai baka labari idan kuka hadu a fili. 
2. Kura a facebook Shi kuran facebook shine wanda duk posting din da yaga anyi, to zai yi comment da kalmar ''LOLs da LMAOs akan komai idan ya gani. 
3. Mai neman suna Shi mai neman suna a facebook shi ne wanda zaka ganshi da abokai wajen 4444 ko fiye, kuma mafi yawa daga cikinsu bai tantance suba, bashi da dalilin abota da su. 
4. Bayin Allah Bayin Allah a facebook sune wadanda akoda yaushe suna yada addinin Allah da yin comment  ga duk wanda yayi post irin nasu koda kuwa ba addininsu daya ba, matukar gaskiya ya fada. 
5. Barawo a facebook Barawon facebook shi ne wanda duk status din da yaga ya burgeshi zai sata yakai shafinsa, ko kuma duk post din da akayi zai dauka zuwa shafinsa amatsayin shi ne yayi. Kuma yanzuma zaiyi abinda ya saba zai dauki wannan ma. Shi baya Share na rubutun wani saidai Copy. 
6. Masoyi a facebook Masoyin facebook shi ne wanda duk post din da yagani saiya danna ''LIKE'' , bazaice komaiba. 
7. Mai kyama a facebook Mai kyama a facebook shi ne wanda duk post din da yagani zaiji bacin rai matukar post din bai shafi bangarensa ba. Kuma zai koma jin haushin mai wannan post. 
8. Mai maganin zaman banza a facebook. Mai maganin zaman banza a facebook shi ne wanda duk rubutun da yagani mai muhimmanci yana karantawa, amma kuma yakan ji haushi idan yaga spelling mistake ko kuma rashin cikakkiyar ma'ana. 
9. Mai Drama a facebook Mai dramar facebook shi ne wanda zai bada labari, amma bazai karasa labarin ba, dan a tambayeshi. Ko kuma magana mai harshen damo d.s. 
10. Mai bandariya a facebook Shi ne wanda zaita kokarin ya farantawa wani rai koda kuwa ransa yana bace, hasalima shi ba'a cikin dariyar yakeba. 
11. Mai neman Labarai Akwai wanda shi kullum yayi ta shared na labarai koda kuwa baisan dalilin labarinba, kuma koda labarin bashida amfani ko ma'ana. 
12. Mai daukar facebook Aiki Akwai wanda ya dauki facebook kamar aiki wanda kullum saiya cewa abokansa na facebook da safe ''Good morning'' kuma kullum saiya rubuta. Dan Allah duk wanda yaga halinsa acikin nan dan Allah yayi hakuri badan cin mutunci nayi shiba. 

DAN GANE DA FACEBOOK (FACT ABOUT FACEBOOK) 

Kamar yadda muka sani facebook ya hada kabilu, yarika, jinsi, ra'ayoyi da akidu kala-kala, wadanda suke amfani da shafin facebook dan gudanar da al'amuransu, facebook ya zama wurin hira mafi karbuwa da yawa aduniya saboda ya ba mai amfani da shi damar da ta dace, wajen tura sako ko posting na abinda ranka yake so, hakan tasa aka yi wannan dan takaitaccen lissafi na facebook. 

SOME FACT ABOUT FACEBOOK 

•.«♣».• A duk inda ka samu mutum 13 bazaka rasa mutum 1 wanda yake facebook ba. 
•.«♣».• 71.2% na masu amfani da intanet a USA suna yin facebook.
 •.«♣».• A duk minti 20 ana shared na Links akan facebook fiye da 1,000,000. •.«♣».• A duk minti 20 akan yi Post a event invite fiye da 1,484,000 million 
•.«♣».• A duk minti 20 ana tagged na Photos fiye da 1,232,000 million a facebook. 
•.«♣».• A duk minti 20 ana Update na status fiye da 1,851,000 million akan facebook 
•.«♣».• A duk minti 20 ana karbar Friend Request fiye da 1.972milion akan facebook. 
•.«♣».• A duk minti 20 ana Uploaded na photos fiye da 2,716,000 millions a facebook. 
•.«♣».• A duk minti 20 ana sent na message fiye da 2,716,000 millions a facebook. 
•.«♣».• A duk minti 20 ana Comments fiye da 10.2 millions a facebook. 
•.«♣».• A duk minti 20 ana rubuta wall post fiye da 1,587,000 million a facebook. 
•.«♣».• Ana Upload na photos fiye da 750millions a hutun sabuwar shekara a facebook. 
•.«♣».• Kashi 48% na matasan America sunce suna samun labaraine ta dandalin facebook. 
•.«♣».• 48% na masu amfani da facebook daga 'Yan shekara 18 zuwa 34 suna duba facebook da zarar sun tashi daga bacci. 
•.«♣».• Mafi yawan masu amfani da facebook yana da wuya ka samu mai abokai kasa da 130. 
•.«♣».• Mutane suna cinye fiye minti 700 billions a duk wata a facebook. 
•.«♣».• 80% na masu amfani da facebook suna hade da facebook page, facebook Group da Event. 
•.«♣».• Akan kirkiri content fiye da 90 a facebook. 
•.«♣».• Ana shared na Content wato (web links, news stories, blog post, Note, Photo Album da sauransu) fiye da 30 billions a facebook duk wata.

1 comments:

Nasiru Abdullahi Take-tsaba said...

๐†๐จ๐๐ข๐ฒ๐š ๐ฆ๐ฎ๐ค๐ž