Thursday 17 November 2022

GYARA MATSALAR RASHIN SAURIN CHAJIN WAYA

Wurin cajin waya yana da hanyoyin lalacewa masu yawa, amma farkon abinda ya kamata gareka kai mai waya shi ne, ta yaya wurin cajin wayarka ya lalace?
Sannan meye dalilin lalacewar sa?
Wacce hanya zaka bi dan kiyaye gaba?
Waɗannan sune tambayoyin da zakayi wa kanka, idan bazaka yiwa kanka irin waɗannan tambayoyin ba, to zakai ta canza waya ko wurin caji, baka samu nasara ba.
Waɗannan sune hanyoyin da suke kawo lalacewar wurin caji, da mafitar magance matsalar

1. AMFANI DA INGANTACCIYAR CAJA WAJEN CHAJI
Yayinda kake buƙatar tabbatar da zaman lafiyar wayarka ko chaji cikin sauri, kuma mai ƙwari dole kana buƙatar cajar waya mai kyau, caja mai kyau tana taka rawar gani matuƙa wajen cin moriyar waya fiye da kima, idan ance caja, ana nufin Ƙundu mai kyau (Charger Adapter), Igiyar caji mai kyau (Original Cable). Indai ka haɗa masu kyau, to ka ɗau hanyar morar wayarka sosai, da caja mai kyau zaka mori
• Chaji mai ƙwari da kuma daɗewa
• Saurin cikar waya da zarar anjona

KUNDU (ADAPTER) Shi ne wanda ake soka shi a allon wuta na bango (Socket), dashi ake chajin waya, kuma ya kasance yana bada wuta dai-dai da waya, idan na wayar ne dole ya zama dai-daitaçiyar wuta yake bayarwa wacce adadinta bai wuce (5 Volt) ba, idan ya wuce 5 to zai bawa waya matsala ko batir, domin tana iya ƙonewa nan take, idan wutar caja ta wuce ɗango 5 da take iya karɓa. Dole a kula da wannan.
Haka shima Cable idan ya samu matsala cajin waya baya sauri, kuma yana kawo lalacewar wurin cajin waya, ka kasa gane kan matsalar gashi yana yi, amma cajin baya taruwa, ko baya taruwa da sauri, matsalar da cable yake haifarwa ga waya
• Rashin saurin caji 
• lalata wurin cajin waya
• Raguwar caji, madadin ya ƙaru.
Idan ka samu kanka acikin matsalar caja, saika canja Cable ka gani, idan baka samu mafita ba saika canja ƙundun cajar.

JIN AKWAI WUTA
Akwai waɗanda suke kashe Cable ɗinsu da kansu basu sani ba, waɗanda suke saka caja abaki su ɗanɗana kafin su jona wayarsu a caji, ko su ɗanɗana Batir dan suji akwai wuta ajikinsa, hakan yana da matsala, domin shi yake lalata wurin cajin waya, domin ramin wurin zaka anshi yayi fari yana gari-gari, zaka ga datti acikinsa, Idan ka kasance kana ɗanɗana waya kafin kasa caji, to ka daina, sannan wayarka, ka samu (Spirit) ka wanke wurin cajin da burushi na wanke baki, zata iya gyaruw, sannan Cable ɗi da kake sawa abaki ka canza shi, domin idan baka canza shi ba, koda wurin cajin wayar ka canza, ba zai daɗe yana yi ba zai sake lalacewa koda baka sa Cable ɗin a baki.
Haka idan batir ne kake ɗanɗanawa, yana lalata ƙafar batir, sannan Batir yana saurin mutuwa, zaka ga yanayin gari takansa, to kana sawa abaki, kum waya zata riƙa mutuwa, sannan zaisa ka riƙa yiwa waya ciko, kusan duk wayoyin da ake musu ciko a batir tanan ya faro, wato ɗanɗana wutar batir.

YAWU:-Yawu, ko Miyau yana da matuƙar cutarwa ga kayan wuta matuƙar yana taɓa su, duk kayan wutar da ake sakawa abaki domin aji aikinsa, to baya ɗaukar lokaci yake lalacewa, misali: Lalacewar wurin cajin waya, lalacewar Cable, Lalacewar batir ko ƙafar batir. Saboda haka mu kula.

CAJI A MOTA
Idan wayarka tana nauyin caji, kuma baka san meye dalili ba, to saika binciki wurin da kake cajin wayarka.
Mota:- Chaji a mota musamman baka amfani da babbar caja, yana riƙe cajin waya ya daina sauri, kuma cajin mota ba'a amfani dashi ku dayawa, saboda kai tsaye indai zaka sa, wanima yazo yasa, to wayarka zataƙi saurin caji, saboda wutar da take zuwa jikin cajar dama wutace dai-dai tacciyar wuta, wacce bata da ƙarfin harba wuta da sauri zuwa wayoyi daban.
Laptop:Masu caji a ajikin computer, ƙarama ko ta girke, suma suna samun matsalar rashin saurin caji, wasu lokutan, abinda zakayi, idan ka samu kankaa wannan matsalar, saika daina caja wayarka ajiki, ka koma caza wayarka acaja zata iya komawa dai-dai.
Solar:-Haka mai cajin waya a solar yana samun matsalar rashin saurin caji wasu lokutan, saboda ita sola tana da matsalar rashin sarrafaffiyar wuta, musamman masu amfani da ƙarama, kuma cajar sola, tana saurin samun matsala, amma zaka ga tanayi, to amma ga matsalar da idan ka gani ka ɗauki mataki.
• Idan wayarka a sola bata saurin caji, ka canza Cable, sannan ba'a ɗanɗana Cable ɗinta yana saurin yin gari
• Rashin ƙwarin caji, idan kana amfani da sola kuma daga baya sai kaga batirinka baya daɗewa to ka binciki batirin domin sola tana saurin kumbuta batir, saboda cajar tana karbar wutar ne dai-dai da yanayi, wani lokacin bata iya riƙe wutar data karɓa ta sarrafata.

DUBA WAYARKA SOSAI
Idan duka waɗancan matakan na sama ba ka amfani da su, ga wasu wayoyin suna amfani da (apps) wanda yake tabbatar da lafiyar wurin caji da caja, misali (Samsung Member apps).

DUBA WURIN CAJI
Aduk lokaxin da zaka saka wayarka a caji ka tabbata ka duba ramin cajin, ko akwai wani datti ko ruwa, idan ruwa ne saika tabbatar ka busar dashi kafin sawa a caji, wasu wayoyin suna nuna alama idan akwai ruwa a wurin cajin wayar, zasu nuna maka.
A irin rashin dubawa anan ake samun matsalar (cajin Error ) ga masu wayoyi masu madannai, sannan masu manya waya suma suna samun (error) ko matsalar kawowa da ɗaukewa.

YANAYIN LOKACI:- Idan ana zafin rana karka saka wayarka caji da zarar ka gama amfani da ita ba, saboda lokacin tayi zafi kana sawa batir zaiyi zafi daganan wata wayar zakaji tana ƙara wata kuma (Battery tempreture) idan ba'a kula ba batir yana iya kumbura, sannan ana iya samun matsalar nauyin caji.

SABUNTA MANHAJA (SOFTWARE UPDATE)
Ka rinƙa sabunta manhajar wayarka da zarar sun sanar dakai ka sabunta, saboda suna dai-daita wayarka, suna cire apps masu nauyi da amfani da caji su baka masu sauƙi, rashin yin update na waya yana iya haifar da matsalar nauyin caji ba tare da ka sani ba.

Sannan ka kula da duk apps da kake amfani dasu, akwai waɗanda suke rikita waya ta daina saurin caji, kuma ta riƙa saurin ƙarewa, idan ka fahimci hakan saika canza su, sannan ka riƙa amfani da apps masu inganci, waɗanda kasan masu kyau ne basu da matsala ko cutarwa. Idan kana buƙatar gane matsalar apps ce, ka kunna wayarka a (Safe mode) zata baka dama ka fahimci matsalar.

BATTERY
Idan kabi duk matakan da suke sama amma baka samu mafita ba, to da yiwuwar batir ɗinka zaka duba matsalar sa ko ka canza wani.
Sannan ana wanke wurin cajin waya da Spirit ko petir marar mis.

0 comments: