Thursday 11 January 2018

SATAR KUDI NA LAYIN MTN

LAYINKA NA MTN SUNA MAKA SATA?


FITA DAGA TSARIKAN MTN NG NA DAUKAN KUDI

Kamar yadda muka sani ne cewa MTN sune na daya a NIGERIA, wajen yawan masu amfani da layikansu, sannan sune na daya wajen tafiyar da hanyar sadarwa ta zamani a Nigeria, sannan duba da yawan masu amfani dasu, hakan tasa masu yi musu korafi sukafi yawa, kuma korafin yana biyo bayan yawan daukar kudin jama'a da sukeyi  ba bisa ka'ida ba, inda su kuma kamfani suke ganin kamar duk wanda yaga kudinsa babu to ba su suka dauka masa haka kawai ba, lallai dole yana wani tsari da suka tanadar kuma suka yanke farashi, inda yayinda kudin ka dake layin idan yayi dai-dai da yadda suke karba sai su dauka su baka bayani akan abinda kake bukata. A bangaren masu  amfani da layin sukan ce basusan da wannan tsarin ba, hasalima basu suka shiga ba,wasu masu amfani da layin na MTN NG na ganin wannan sata ce, domin wasummu basu da masaniya akan shiga tsari,wasuma basu san tsarin da layinsu yake ciki ba, amma sukan ga anyi musu sama da fadi da wani kaso na daga abinda suka sa. Al'umma na ganin hakan saka ci ne daga jagorori, wasu kuma na zargin toshiyar baki ne da ake ba jagororimmu tasa sukayi halin ko in kula, da wannan matsala, wasu kuma na ganin ai su manya ba'a dauka musu nasu, kalamai kowa da irin nasa.

Babban abinda yake batawa masu amfani da layin MTN rai shi ne;






1
Yawan satar kudi da ake yiwa mafi yawa daga masu amfani da layin, wasu idan suka sa kati kamar na N100, kafin su kira andauke musu rabin kudin ko kuma adauki N70 abar maka N30, kai kuma a wannan lokacin tsarin wayarka na  N100 ne, wani a dari dimma takaitawa zaka yi yanzu kuma saura N30 ko N50, wani kuma bayan minti kadan da sa katin zaiga babu ko naira sun dake duka, hakane yake ta faruwa da masu amfani da MTN NG. haka zaka hakura ka dawo sa katin N50 da tunanin zaka tsira ganin cewar kana sawa kadan, wato kafin su dauka ka cinye, anamma ba zasu barka ba, zasu tana dar maka tsari dai-dai da abinda kake sawa, wato sai su koma daukar kamar N10, N20, da sunan matsakaiciyar bukata (mSERVICE), ko kuma su rika daukan N25 da sunan tsarikan mega byte na zaurukan sada zumunta, badai zasu barka ka ajiye komai alayinka ba.





2
KORAFINKA BAYA KARBUWA

Masoyin layinsa, kuma masoyin masu mu'amala dashi yakanyi kafa-da-kafa zuwa kamfani mafi kusa dashi domin samun masalaha, kan cewar bazai juri amfani da layin a wannan matakin ba, yana bukatar a fitar dashi daga duk wani tsari  na daukan kudi, zasu nuna masa cewar zasu cire, amma a hakikanin gaskiya sai kaga wasu basa cire musu, wani yakan je kamfani sau biyu, amma bai samu nasara sun cire ba, hakan ya biyo bayan raina mu da sukayi kan cewar masu amfani da layinsu ba zasu iya rabuwa da layin ba. Duk wanda Allah ya bashi shikimar sarrafa waya koda ajiye lamba da gogewa ya iya to tabbas yana samun wadanda suke kawo masa korafi akan cewar ana dauke musu kudi alayikansu, da ga karshe idan yayi bai yiba sai yace ka kira kamfani, wanda suma ba gyarawa suke yi ba.





3
Wani abun ban takaicin ma shi ne, duk wani sako da ake turawa zuwa wasu labobin domin tsayarwa, to  idan ka kasance baka UPDATE da UPGRADE na sanin da kayi musu saika tsunduma sabon tsari akokarin fita daga wani, misali kamar kana tsarin CALLERTUNE kuma kana son fita ada can baya idan ka tura kalmar "CANCEL" zuwa 4100 zasu cireka, amma yanzu, bah aka bane.



DAKATAR DA WASU DAGA TSARIKAN MTN PLAY NIGERIA (STOP MTN PLAY)

Wasu aduk lokacin da suka sa kati alayinsu na MTN ana dauka musu kudi, wasu yanzu haka sun sallami layin MTN, sun canza wani, wannan halin ya biyo bayan tsarin su na MTN PLAY wanda da shi suke amfani suke zalintar al'ummar kasa, wanda irin wadannan tsarikan suna wahalar fita, wasuma sun gaji da kiran kamfani, da tuntubar masana na kusa.
Wannan hanya ce da zata taimaka wajen cire tsarin MTN PLAY, shi tsarin yana kunshe da duk wani bayani da kake samu daga kamfanin MTN.

Abubuwan da suke karkashin MTN PLAY sune
* Labarun wasanni, ko na Club dinka da kake sport.
* Labarun siyasa
* Labarun yau da kullum kamar yanayin farashin kasuwa da sauransu.
* Labaru na musamman, daga tashoshi kamar CNN, BBC, Aljazeera, da sauran wurare na labarai.
* Labarun koyon harsuna kamar English
* Da sauran abubuwa kamar karin magana.


Wannan shi ne jerin wasu daga tsarin MTN PLAY da yadda zaka fita


S/NO

SUNAN TSARI

SALON SAKO

FARASHI

YADDA ZAKA FITA

01
MTN MTV
. Idan kana samun sakon suna dauka maka
N50
tura UMTV zuwa 700

02
MTN Newspaper LindaIkeji
MTN Newspaper na LindaIkeji Monthly suna cire
N120
tura "NO LIM" zuwa 4900

03
MTN Newspaper na Genevieve Magazine
MTN Newspaper na Genevieve Magazine Monthly suna cire
N120
tura "NO GMM" zuwa 4900

04
MTN Newspaper na Sensce Recritment
MTN Newspaper na Sensce Monthly suna cire
N120
tura "NO SRM " zuwa 4900

05
MTN Newspaper na WOW Magazine
MTN Newspaper na WOW Magazine Monthly suna cire
N120
tura "NO WMM" zuwa 4900

06
MTN Newspaper na Business Day Finance
MTN Newspaper na Business Day Finance Monthly suna cire
N120
tura "NO BDM " zuwa 4900

07
MTN Newspaper na City People Entertainment
MTN Newspaper na City People Entertainment Monthly suna cire
N120
tura "NO CPM" zuwa 4900

08
MTN Newspaper na International Sport
MTN Newspaper na International Sport Monthly suna cire
N120
tura "NO ISM" zuwa 4900

09
MTN Newspaper na Complete Sport
MTN Newspaper na Complete Sport Monthly suna cire
N120
tura "NO CSM" zuwa 4900

10
MTN Newspaper na " Vanguard News
MTN Newspaper na " Vanguard News Monthly suna cire
N120
tura "NO VNM " zuwa 4900

11
CNN NEWS
Samun labaran CNN zasu rika dauka maka N50,
N50
Tura UFCNN zuwa 700.


12
 LEARNING English
Idan kana samun labaran English zasu rika. Dauka maka,
 N50 ko N100  duk sati
tura "ULEN zuwa 700.

13
MTN Newspaper na "Internationl News
samunlabaran MTN Newspaper na "Internationl News Monthly suna cire
N120
tura "NO INM zuwa 4900

14
MTN Dating
. Domin fita daga MTN Dating

tura "STOP zuwa 44076

15
Chelsea FC
samun labaran Chelsea FC zasu rika daukar
N50
tura "UCFC zuwa 700.

16
Quick Facebook service
salon Quick Facebook service, ana dauka musu  N25 a sati N5 kullum ka danna *510*22# domin saida shi.
N100
ka danna *510*22#