Thursday 11 January 2018

WINDOWS PHONE UPGRADE ZUWA WINDOWS 10


YADDA ZAKA SABUNTA MANHAJAR WINDOWS PHONE 
(WINDOWS PHONE UPGRADE)



Ga wadanda suke da waya mai dauke da manhajar windows, suna sane da yadda kamfanin Microsoft yake samar musu da ci gaba ta fiskar masarrafar zamani, sannan suke fitar da sabbin manhaja lokaci bayan lokaci, aduk lokacin da lokacin sabuntawa yayi, wasu sukan yi UPDATE daga kan waya ta cikin Setting, Phone update, amma yin Upgrade ba kowa yake iya yinsa daga kan waya ba, a wannan darasin zamu gabatar da yadda zakayi Upgrade da kanka ba tare da ka hada wayarka da computer ba.
Zamu gabatar da yadda ake sabunta manhajar windows ne zuwa windows 10.

YADDA ZAKA SABUNTA MANHAJAR WINDOWS PHONE ZUWA WINDOWS 10 DA
(Windows 10 Upgrade Advisor)

Idan kana bukatar sabunta manhajar windows zuwa 10 saika bi wadannan matakan,
1.      Ka kunna windows phone dinka, saika latsa “Windows app store” ko “Market place” saika latsa alamar bincike (Search) ka rubuta “Upgrade advisor” saika sauko dashi kan wayar taka.

>.  Domin amfani da “Upgrade advisor” dole manhajar da kake amfani da ita ya  zama takai  “Version 8” kafin yunkurinka na windows 10, domin duba windows version dinka, kaje “<Settings <about> more information>”

>. Bayan ka saukar da UPGRADE ADVISOR akan wayarka, saika bude shi, zai baka allo na biyu saika latsa    next    

>. Zai duba cancantar wayarka akan sabunta manhaja “Checking for updates
Shin wayarka zata yi upgrade zuwa windows 10? Idan bazata yi ba ko kuma akwai matsala anan zata nuna maka, yayin da ta gama checking update saita nuno maka Upgrade available

Mataki na karshe zata saukar maka da windows 10 akan wayarka, idan t agama saika latsa
Done

KASANI:- Matukar wayarka windows 8.0 ne akanta, to windows 10 bazai sauka akan wayarka ba, ka lura da duk bayanan da Upgrade advisor zai nuna maka, amma idan version na windows dinka 7+ ne, to wannan application bazai yi install akan wayarka ba, koda kayi “search a app store ko market place,” zata nuna maka batasan abinda kake nema ba.

0 comments: