Thursday 11 January 2018

9mobile/etisalat INTERNET SETTING


YADDA ZAKA SAITA ANDROID PHONE TA RIKA BROWSE DA LAYIN 9mobile/etisalat


Layin 9mobile wanda aka fi sani da etisalat, yana daya daga cikin layika da ake mu’amala dasu ta harkar yanar gizo, kuma akan sami wani yana samun matsalar amfani da nasa, musamman matsalar setin “INTERNET CONNECTION” wannan shi ne dan bayani akan yadda zaka saita layinka a browse kai da kanka.
Akwai hanyar setin internet alayinaka na 9mobile guda biyu.

1.   Akwai seti na kai tsaye daga kamfani, wanda zasu turo maka, bukatarsu kawai ka saukar dashi cikin wayarka, “Install” kana saukar dashi nan take zaka fara shiga yanar gizo.
Domin samun wannan seti kai tsaye kaje akwatin sako na wayarka  “Message  ka rubuta  “SETTINGS” ka tura zuwa 790.



KASANI:- Wannan matakin sako na musamman ba’a kowacce irin waya yake aiki ba, zaka iya turawa, amma kaga basu turo maka sakon ba suna, amfani ni ne da wasu wayoyin ba’a kowacce ba. Sannan basa bukatar “PIN” yayin “Install na Configuration” idan kuma sun bukaci kasa “PIN  a wayarka saika sa “0000”.

YADDA ZAKA SHIGAR DA SETIN INTERNET NA 9mobile DA KANKA A ANDROID PHONES
Wannan matakin shi ne wanda zaka shigar da setin da kanka ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda muka sani akwai wayoyi kala-kala, sannan ma bam-banta tsarin setin shiga yanar gizo,


Android 1, kaje “Settings, latsa “All Setting <more setting >Mobile Network > Access Point Name.
Android 2 kaje “Settings >Wireless & Network> Mobile Network> Access Point Name
Android 3 Kaje “Settings > network & more/ Genaral settings > Access Point name
Vivo android kaje “Settings >General> Network> Access Point Name
Ya danganta da kalar android dinka saika duba dai-dai da mashigar wayarka, saika shigar da wannan setin

Account Name:-      9mobile
Access Point Name (APN):_   9mobile
Username:-      karka sa komai a wurin (Leave it blank)
Password:-      karka sa komai a wurin (Leave it blank)
Proxy Port:-     010.071.170.005
Port:-              8080
Homepage:_         https://www.mobile.9mobile.com.ng

Authenticative:-    PAP

0 comments: