Monday 21 December 2020

YADDA ZAKA GANO LAMBOBINKA NA KATIN DAN KASA, BAYAN KATINKA YA ƁATA KO BAKA GANSHI BA,

Yana iya yiwuwa, kana da katin ɗan kasa, ka rasa inda ka sa shi, wani ma nasa ya ɓata, to ga yadda zaka yi ka samu Serial Number ɗinsa, cikin sauki basai ka sake yin wani ba, domin haɗa shi da lambar wayarka.

1. Ka tabbata kaine ka yi rijistar sa.

2. Ka tabbata layinka daka yi rijistar katinka na dan kasa yana aiki, wato alokacin rijista anbuƙaci lambar wayarka, to ita wannan lamba daka bayar ka tabbata tana aiki yanzu, kuma tana kusa da dakai.

Koda bata wurinka, matukar kana kiranta zaka iya rokon arziki ya taimakeka, ya duba maka,

3. Idan layin yana wurinka ka danna *346# nan take zasu turo maka da lambobin da ake bukata a wannan lokaci.

Idan layin naka ya ɓata to bazai yi da sabon layinka ba, matukar bada shi kayi katin Ɗan ƙasa ba.

0 comments: