Monday 26 March 2018

AMFANIN DA ZAUREN SADA ZUMUNTAR DA BAYAYI A NAHIYARKA

Idan ka samu kanka kana bukatar wani zauren sada zumunta bana yankin ka ba, sannan kuma bayayi a yankinka, kwata-kwata, dalili badan yankinka akayi shiba, sannan kai kuma kaji kana bukatar mu'amala dashi, ko ka hadeshi da zauren sada zumunta kamar instagram, saika bi wadannan matakan na kasa:

Misali mu dauki Mixi account, shi wannan shima dandalin sada zumunta ne amma na yankin Japan ne kadai, kenan kaga wanda baya yankin Japan to bazai mallaki shi wannan account na Mixi ba, saboda wayarka ce ta ce musu ba'a yankinsu kake ba, wato anan setin da wayarka take dauke dashi shi ne,  setin agogo bana yankinsu bane, sannan shi kansa yankin ka ba nasu bane (Region) sannan yarenka ba nasu bane.
Idan kana bukatar amfani da irin wadannan zauruka saika bi wannan matakin

1. Kaje phone's Settings saika latsa  General > International > Region Format. Saika zabi  Japanese (Japan) 
Kana maida shi, shikenan kaje ka budeshi nan take zai bude,  kuma koda kana bukatar hadashi da wasu zaurukan idan kaje setin dinsu zaka ganshi awurin, misali kamar kana bukatar ka hada shi da Instagramzaka ganshi.

Abu na biyu shi ne kamar weibo shima yana yine a yankin kasar China, idan ka duba Vivo, Oppo, Lenovo ko wasu daga GiONEE zaka samu wadannan zauruka acikinsu, tunda dama wayoyin wasu daga cikinsu na kasar China ne da nahiyarsu. Saika bi wadannan matakan shima

1. Kaje  phone's Settings saika taba General > Language & Region > awurin da akasa  Region saika zabi Chinese ko dai wata kasar da take nahiyar (China, Taiwan da sauransu)  saika latsa DONE, idan ka dawo ka bude shi zaiyi aiki nan take, ko kuma idan kana bukatar hadashi da zauren sada zumunta, kamar instagram.
Duka zaurukan sada zumunta Facebook, Twitter ko Instagram ba kowanne yake da sauki kamarsu ba, saboda su duniya ce. Sai wasu kasashen da basa ta'ammali dasu ko yi musu iyaka.

ABIN LURA:-
Canza yanki da yare, bazai canza yaren da kake amfani dashi akan wayarka ba, kawai dai zai canza nahiyarka da kuma setin agogo,  amma yaren da kake amfani dashi yanan bai canza ba, kawai yaren nahiya da nahiyar kanta ka canza, amma ba yarenka na mu'amalarka da waya, wannan salon shi kabi ga duk wani zauren sada zumunta da kake bukatarsa na kowacce kasa, saika zabi yankinsu.