Monday 21 December 2020

 YADDA ZAKA HAƊA LAYINKA NA MTN DA KATIN ƊANKASA


Kamar yadda sanarwa ta fita daga Gwamnatin tarayya, ta ma'aikatar sadarwa, "Nigerian Communication Commission" (NCC) cewar akwai bukatar duk ɗan Nigeria, daya tabbatar ya hada layin wayar sa da Katin sa na ɗan kasa, domin tabbatar da tsaro, sannan aka bada ƙaramin wa'adi, kan cewar duk wanda bai aiwatar ba, zai iya jin layinsa akulle, sati biyu akaba duk ɗan kasa, daya tabbata yayi wannan hadin.

Ɗaya daga cikin gudun mawar da kamfanin layi suka taimaka domin rage cunkoso shi ne kowa zai iyayi daga gida basai ka ziyarci ofishinsu ba, matukar kana da katin ɗankasa, wannan shi ne na MTN

1. Ka tabbata layinka MTN ne.

2. Ka tabbata kana da katin Ɗan kasa, kuma yana hannunka

3. Akan layinka na MTN saika danna *785# ko *789#.

Zasu baka allo, cewar ka shigar da lambar mallakar katin dan kasa "NIN Serial Number) guda goma sha daya ce. 


Wannan shi ne hanya mafi sauki da zaka tseratar da layinka daga kullewa, kuma zuwa 30 ga watan 12, na wannan shekarar da muke ciki 2020. Ka gaggauta yi domin tsira da layinka.

0 comments: