LAYINKA NA MTN SUNA MAKA SATA?
FITA DAGA TSARIKAN MTN NG NA
DAUKAN KUDI
Kamar yadda muka sani ne
cewa MTN sune na daya a NIGERIA, wajen yawan masu amfani da layikansu, sannan
sune na daya wajen tafiyar da hanyar sadarwa ta zamani a Nigeria, sannan duba
da yawan masu amfani dasu, hakan tasa masu yi musu korafi sukafi yawa, kuma
korafin yana biyo bayan yawan daukar kudin jama'a da sukeyi  ba bisa ka'ida ba, inda su kuma kamfani suke
ganin kamar duk wanda yaga kudinsa babu to ba su suka dauka masa haka kawai ba,
lallai dole yana wani tsari da suka tanadar kuma suka yanke farashi, inda
yayinda kudin ka dake layin idan yayi dai-dai da yadda suke karba sai su dauka
su baka bayani akan abinda kake bukata. A bangaren masu  amfani da layin sukan ce basusan da wannan
tsarin ba, hasalima basu suka shiga ba,wasu masu amfani da layin na MTN NG na
ganin wannan sata ce, domin wasummu basu da masaniya akan shiga tsari,wasuma
basu san tsarin da layinsu yake ciki ba, amma sukan ga anyi musu sama da fadi
da wani kaso na daga abinda suka sa. Al'umma na ganin hakan saka ci ne daga
jagorori, wasu kuma na zargin toshiyar baki ne da ake ba jagororimmu tasa
sukayi halin ko in kula, da wannan matsala, wasu kuma na ganin ai su manya ba'a
dauka musu nasu, kalamai kowa da irin nasa.
Babban abinda yake batawa
masu amfani da layin MTN rai shi ne;
1 
 | 
  
Yawan satar kudi da
  ake yiwa mafi yawa daga masu amfani da layin, wasu idan suka sa kati kamar na
  N100, kafin su kira andauke musu rabin kudin ko kuma adauki N70 abar maka
  N30, kai kuma a wannan lokacin tsarin wayarka na  N100 ne, wani a
  dari dimma takaitawa zaka yi yanzu kuma saura N30 ko N50, wani kuma bayan
  minti kadan da sa katin zaiga babu ko naira sun dake duka, hakane yake ta
  faruwa da masu amfani da MTN NG. haka zaka hakura ka dawo sa katin N50 da
  tunanin zaka tsira ganin cewar kana sawa kadan, wato kafin su dauka ka cinye,
  anamma ba zasu barka ba, zasu tana dar maka tsari dai-dai da abinda kake
  sawa, wato sai su koma daukar kamar N10, N20, da sunan matsakaiciyar bukata
  (mSERVICE), ko kuma su rika daukan N25 da sunan tsarikan mega byte na
  zaurukan sada zumunta, badai zasu barka ka ajiye komai alayinka ba. 
 | 
 
2 
 | 
  
KORAFINKA
  BAYA KARBUWA 
Masoyin layinsa, kuma masoyin masu mu'amala
  dashi yakanyi kafa-da-kafa zuwa kamfani mafi kusa dashi domin samun masalaha,
  kan cewar bazai juri amfani da layin a wannan matakin ba, yana bukatar a
  fitar dashi daga duk wani tsari  na daukan kudi, zasu nuna masa cewar zasu
  cire, amma a hakikanin gaskiya sai kaga wasu basa cire musu, wani yakan je
  kamfani sau biyu, amma bai samu nasara sun cire ba, hakan ya biyo bayan raina
  mu da sukayi kan cewar masu amfani da layinsu ba zasu iya rabuwa da layin ba.
  Duk wanda Allah ya bashi shikimar sarrafa waya koda ajiye lamba da gogewa ya
  iya to tabbas yana samun wadanda suke kawo masa korafi akan cewar ana dauke
  musu kudi alayikansu, da ga karshe idan yayi bai yiba sai yace ka kira
  kamfani, wanda suma ba gyarawa suke yi ba. 
 | 
 
3 
 | 
  
Wani abun ban takaicin ma shi ne, duk wani sako da ake turawa
  zuwa wasu labobin domin tsayarwa, to  idan ka kasance baka UPDATE da UPGRADE na
  sanin da kayi musu saika tsunduma sabon tsari akokarin fita daga wani, misali
  kamar kana tsarin CALLERTUNE kuma kana son fita ada can baya idan ka tura
  kalmar "CANCEL" zuwa 4100 zasu cireka, amma yanzu, bah aka bane. 
 | 
 
DAKATAR DA WASU DAGA TSARIKAN
MTN PLAY NIGERIA (STOP MTN PLAY)
Wasu aduk lokacin da
suka sa kati alayinsu na MTN ana dauka musu kudi, wasu yanzu haka sun sallami
layin MTN, sun canza wani, wannan halin ya biyo bayan tsarin su na MTN PLAY
wanda da shi suke amfani suke zalintar al'ummar kasa, wanda irin wadannan
tsarikan suna wahalar fita, wasuma sun gaji da kiran kamfani, da tuntubar
masana na kusa.
Wannan hanya ce da zata
taimaka wajen cire tsarin MTN PLAY, shi tsarin yana kunshe da duk wani bayani
da kake samu daga kamfanin MTN.
Abubuwan da suke karkashin MTN PLAY sune
* Labarun wasanni, ko na
Club dinka da kake sport.
* Labarun siyasa
* Labarun yau da kullum
kamar yanayin farashin kasuwa da sauransu.
* Labaru na musamman,
daga tashoshi kamar CNN, BBC, Aljazeera, da sauran wurare na labarai.
* Labarun koyon harsuna
kamar English
* Da sauran abubuwa
kamar karin magana.
Wannan shi
ne jerin wasu daga tsarin MTN PLAY da yadda zaka fita
S/NO 
 | 
  
SUNAN
  TSARI 
 | 
  
SALON
  SAKO 
 | 
  
FARASHI 
 | 
  
YADDA
  ZAKA FITA 
 | 
 
01 
 | 
  
MTN MTV 
 | 
  
. Idan kana samun sakon suna dauka
  maka 
 | 
  
N50 
 | 
  
tura UMTV zuwa 700 
 | 
 
02 
 | 
  
MTN Newspaper LindaIkeji 
 | 
  
MTN Newspaper na LindaIkeji
  Monthly suna cire 
 | 
  
N120 
 | 
  
tura "NO LIM" zuwa 4900 
 | 
 
03 
 | 
  
MTN Newspaper na Genevieve
  Magazine 
 | 
  
MTN Newspaper na Genevieve
  Magazine Monthly suna cire 
 | 
  
N120 
 | 
  
tura "NO GMM" zuwa 4900 
 | 
 
04 
 | 
  
MTN Newspaper na Sensce Recritment 
 | 
  
MTN Newspaper na Sensce Monthly
  suna cire 
 | 
  
N120 
 | 
  
tura "NO SRM " zuwa 4900 
 | 
 
05 
 | 
  
MTN Newspaper na WOW Magazine 
 | 
  
MTN Newspaper na WOW Magazine
  Monthly suna cire 
 | 
  
N120 
 | 
  
tura "NO WMM" zuwa 4900 
 | 
 
06 
 | 
  
MTN Newspaper na Business Day
  Finance 
 | 
  
MTN Newspaper na Business Day
  Finance Monthly suna cire 
 | 
  
N120 
 | 
  
tura "NO BDM " zuwa 4900 
 | 
 
07 
 | 
  
MTN Newspaper na City People
  Entertainment 
 | 
  
MTN Newspaper na City People
  Entertainment Monthly suna cire 
 | 
  
N120 
 | 
  
tura "NO CPM" zuwa 4900 
 | 
 
08 
 | 
  
MTN Newspaper na International
  Sport 
 | 
  
MTN Newspaper na International
  Sport Monthly suna cire 
 | 
  
N120 
 | 
  
tura "NO ISM" zuwa 4900 
 | 
 
09 
 | 
  
MTN Newspaper na Complete Sport 
 | 
  
MTN Newspaper na Complete Sport
  Monthly suna cire 
 | 
  
N120 
 | 
  
tura "NO CSM" zuwa 4900 
 | 
 
10 
 | 
  
MTN Newspaper na " Vanguard
  News 
 | 
  
MTN Newspaper na " Vanguard
  News Monthly suna cire 
 | 
  
N120 
 | 
  
tura "NO VNM " zuwa 4900 
 | 
 
11 
 | 
  
CNN NEWS 
 | 
  
Samun labaran CNN zasu rika dauka
  maka N50, 
 | 
  
N50 
 | 
  
Tura UFCNN zuwa 700. 
 | 
 
12 
 | 
  
 LEARNING English 
 | 
  
Idan kana samun labaran English
  zasu rika. Dauka maka, 
 | 
  
 N50 ko N100  duk
  sati 
 | 
  
tura "ULEN zuwa 700. 
 | 
 
13 
 | 
  
MTN Newspaper na
  "Internationl News 
 | 
  
samunlabaran MTN Newspaper na
  "Internationl News Monthly suna cire 
 | 
  
N120 
 | 
  
tura "NO INM zuwa 4900 
 | 
 
14 
 | 
  
MTN Dating 
 | 
  
. Domin fita daga MTN Dating 
 | 
  
tura "STOP zuwa 44076 
 | 
 |
15 
 | 
  
Chelsea FC 
 | 
  
samun labaran Chelsea FC zasu rika
  daukar 
 | 
  
N50 
 | 
  
tura "UCFC zuwa 700. 
 | 
 
16 
 | 
  
Quick Facebook service 
 | 
  
salon Quick Facebook service, ana
  dauka musu  N25 a sati N5 kullum ka danna *510*22# domin saida shi. 
 | 
  
N100 
 | 
  
ka danna *510*22# 
 | 
 
1 comments:
Muna godiya
Post a Comment