Tuesday 23 January 2018

YADDA ZAKA MALLAKI GMAIL ACCOUNT

Domin shiga Google products kamar YouTube, Google Play, da Google Drive sannan da cin gajiyar muhawara daga google+ ko GTalk,  dole kana bukatar mallakar Username da password,  kafin fara amfani da daya daga cikin wadannan, akwai hanyar mallakar gmail guda biyu.

1. ka ziyarci shafin mallakar gmail saika latsa Create gmail Account ko kayi amfani da google ka tambayi, "create gmail account".



2. Zasu baka allon da zaka cike, domin mallakar gmail account dinka,
3. Kabi a hankali wajen cike form din, ka kuma sa lura.


KASANI:- Wajen mallakar username dinka, ka lura da wadannan abubuwan
1. Matukar username dinka daka shigar,  wani ya shigar dashi kafin kai to naka bazai yi ba.
2. Idan username daka shigar yayi kusan iri daya dana wani, to naka bazai yiba, misali talala@gmail.com shi ne wanda aka bude naka ya zama talala@gmail.com,  to naka bazai yi ba.  saboda sunyi kala.
3. Idan username da zaka bude wani abaya ya bude,  daga baya kuma ya goge namma naka bazai yi ba,  saboda yana masarrafar google.
4. Idan sunan da zaka bude dashi,  wani yayi report dinsa, akan cewar zai dameshi, to namma naka bazai budu ba.

Idan akwai wani da yake amfani da google dinka,  ko kuma yana amfani da  sunanka saika ziyarci Internet crime Complaint domin daukar mataki akansa nan take.