Wednesday 21 March 2018

SETA BLACKBERRY A BROWSING DA AIRTEL NG

Idan ka mallaki layin airtel NG, kuma kana bukatar yin browsing da shi, to dole yana bukatar seti, sannan abu mai muhimmanci wajen seta layin Airtel NG shi ne Access Point Name (APN) dole lallai ka tabbata kasa APN din dai-dai, rashin sashi dai-dai ka iya haifar da matsalar shiga yanar gizo, domin yana iya haifar da rashin saurin budewa, ko kuma rashin buduwar data gaba daya yadda APN din yake shi ne internet.ng.airtel.com
Sannan baya bukatar Username da password, akwai wadanda suke saka "internet"  amatsayin username da password wannan airtel baya bukata, idan ya kasance kasa shi, to bazaka yana saurin bude shafi ba, amma zaiyi koda shi, amma ka bar wurinsa ba komai yafi saurin yi.

Kuma shi Airtel yana da tsarin saiti na kai tsaye (Automatic Configuration) kuma shi ba kowacce waya take samun sa'arsa ba, kuma mafi yawa yakan sauka ne da tsohon tsarin zain,  wato APN:- internet.ng.zain.com, kuma yakan zo da username da password, wannan baya sauri, sannan yanayin wurin shigar da kowanne seti yana da bam-banci, wato tsari da wurin seta internet a Android Phones,  Symbian/Java Phones,  iPhones/iPad ko  Windows Phones duka da bam-banci, latsa daya daga cikin sunayen wayoyin domin kaga yadda zaka saita taka.
Domin seta layinka na airtel ya rika browsing akan BlackBerry dinka, ya danganta da kalar BB dinka, tunda ita ma kala-kala ce,  sannan kalolinta ya danganta da irin matakin manhajar da take dauke da ( OS version) 

Idan kana amfani da OS 7, misali BB Bold 5, saika je Options>Device and Status information>Advanced System settings>TCP/IP> saika latsa APN settings enabled>
Saika shigar da settings da dake kasa.


Idan kuma OS 5 ce dakai misali  BB Bold 2 saika latsa Options>Advanced Options>TCP/IP> Saika latsa APN settings enabled> sannan ka latsa APN> ka shigar da settin dinka.


ACCOUNT NAME:- Airtel NG                                            ...    
APN:-                     internet.ng.airtel.com                        ...  
USERNAME:-        Karka rubuta komai (Leave it blank)
PASSWORD:-        Karka rubuta komai (Leave it blank)
IP/PROXY:-            Karka rubuta komai (Leave it blank)
PORT:-                   Karka rubuta komai (Leave it blank)
HOMEPAGE:-       www.ng.airtel.com                             ...    

0 comments: