Idan ka mallaki layin airtel NG, kuma kana bukatar yin browsing da shi, to dole yana bukatar seti, sannan abu mai muhimmanci wajen seta layin Airtel NG shi ne Access Point Name (APN) dole lallai ka tabbata kasa APN din dai-dai, rashin sashi dai-dai ka iya haifar da matsalar shiga yanar gizo, domin yana iya haifar da rashin saurin budewa, ko kuma rashin buduwar data gaba daya yadda APN din yake shi ne internet.ng.airtel.com
Sannan baya bukatar Username da password, akwai wadanda suke saka "internet" amatsayin username da password wannan airtel baya bukata, idan ya kasance kasa shi, to bazaka ga yana saurin bude shafi ba, amma zaiyi koda shi, amma ka bar wurinsa ba komai yafi saurin yi.
Kuma shi Airtel yana da tsarin saiti na kai tsaye (Automatic Configuration) kuma shi ba kowacce waya take samun sa'arsa ba, kuma mafi yawa yakan sauka ne da tsohon tsarin zain, wato APN:- internet.ng.zain.com, kuma yakan zo da username da password, wannan baya sauri, sannan yanayin wurin shigar da kowanne seti yana da bam-banci, wato tsari da wurin seta internet a Symbian/Java Phones, iPhones/iPad, BlackBerry, ko Windows Phones duka da bam-banci, latsa daya daga cikin sunayen wayoyin domin kaga yadda zaka saita taka.
Domin seta android dinka saika bi wadannan matakan
Settings >More Settings>Mobile Network>Access Point Names>saika latsa Menu options> New APN>
ACCOUNT NAME:- Airtel NG ...
APN:- internet.ng.airtel.com ...
USERNAME:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
PASSWORD:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
IP/PROXY:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
PORT:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
HOMEPAGE:- www.ng.airtel.com ...
Authentication type:- PAP ...
Wednesday, 21 March 2018
Related Posts:
SETA WINDOWS PHONE TAYI BROWSING DA AIRTEL NG Idan ka mallaki layin airtel NG, kuma kana bukatar yin bro… Read More
INTERNET SETTING AKAN iPhone, iPad DA AIRTEL NG Idan ka mallaki layin airtel NG, kuma kana bukatar yin bro… Read More
SETA LAYIN AIRTEL NG A BROWSING AKAN ANDROID Idan ka mallaki layin airtel NG, kuma kana bukatar yin browsing da s… Read More
SETA INTANET AKAN SYMBIAN KO JAVA DA AIRTEL NGIdan ka mallaki layin airtel NG, kuma kana bukatar yin brows… Read More
0 comments:
Post a Comment