Monday 5 March 2018

YADDA ZAKA KARE WAYARKA DAGA BARAYI

Ga wadanda suke da android suna fiskantar satar wayar, hakan ya biyo bayan saboda ba'a kama su ne, ko kuma ba'a bi-bi-yarsu, ta yadda idan mutum ya dauki wayarka to bazai kara ba, domin daukar mataki ka bi wadannan matakan.

Kaje Settings >
Security >
Mobile Anti-theft


Idan ka latsa shi zai baka inda zaka shigar da bayananka, idan kuma wayar taka ba sabuwa ka siya ba, me yiwuwa wani yayi abaya akanta, ko kuma kaine kayi, to zai baka zabi guda biyu, Previous Setting, da New Settings,
Idan ka zabi Use previous setting to tsohon na baya zai koma, matukar ba kaine wanda ka fara seta shi ba, to ka zabi Setup New settings, idan ka zabi Setup New settings saika bi wadannan matakan.

1. Ka shigar da PIN dinka,  amfanin shi wannan PIN da zaka shigar shi ne, duk lokacin da wani ya dauki wayarka, ya cire maka layinka, yasa nasa to bazata sarrafu ba, har sai anshigar da wannan lambobi daka shigar mata, kenan babu mai cire maka layi yayi amfani da wayarka saika sani, sannan kuma PIN din da kasa anan aikinsa anan ne kadai, pattern, password, ko PIN daka shigar na kulle wayarka bashi da alaka da wannan. lallai kuma ya zama daga 6 zuwa 12,karyayi kasa da 6 kuma karya wuce 12.

2. Anan kuma saika shigar da lambar wayar waninka, wato yayinda wani ya dauki wayarka, yana layinsa aciki, nan take za'a turo lambar wayar da aka sa akan wayar taka, misali kana da layin MTN sai aka cire layin naka, aka sa wani daban, kai kuma kasa lambar yayanka ko ta kaninka, kota matarka, ko ta mahaifiyarka, lambar da kasan baka tare da ita, zasu tura sako zuwa wannan lambar da kasa da cewar, wayar wane akwai yiwuwar wayar wane an dauke ta, sannan kuma da lambar da aka dora akan wayar taka da ita za'a yi wannan sakon. kana iya saka lambobin mutum uku, saboda yanayin rashin chajin wata, ko kulawar waninka akan waya. 


3. Bayan ka tabbatar wayar nan  taka dauketa akayi, to zaka iya sarrafa wayarka yadda kake so, kana iya kulle ta, ko ka go ge kanta, kana iya yin Backup na kayan ciki kabar masa wayar, kana iya bibiyarsa, idan kuma na gida ne, kana iya amfani da lambar wayar ko cigiyarta cikin lambobin abokai domin tabbatar da barawon na gida ne. 

0 comments: