Thursday, 22 February 2018

YADDA ZAKA KOMA TSOHON WINDOWS DINKA BAYAN KAYI UPGRADE (Windows downgrade)
Bayan sabunta manhajar Windows 10 (Windows 10 UPGRADE), saboda wani dalili naka na sabuntawa,  sai kuma kaga kafin jin dadin tsohon windows da kake amfani dashi, kuma gashi ka koma Windows 10, anan zamu gabatar da yadda ake komawa tsohon windows dinka "Rolling back to previous Windows" 
Ana iya komawa Windows na baya ne kawai, acikin kwana talatin da yin "Upgrade"  wato kana da zabi tsakanin kwana talatin na yiwuwar ci gaba da sabon Windows kokuma komawa naka na baya. domin komawa tsohon windows dinka saika bi wadannan matakan
1. Ka kunna computer dinka,  a Windows 10 dinka saika latsa Start Menu,
sannan ka latsa Settings.
2. Idan ka latsa Settings, zai baka allo na gaba saika zabi Update & Security

3. Idan ka latsa Update & Security zai baka allo na gaba,  anan saika latsa Recovery zai baka abinda yake dauke dashi,  anan zai baka bayani saika latsa Go back to Windows anan duk kalar windows dinda kake dashishi zai baka, idan kana amfani da Windows 8 abaya ko windows 7, zai nuna maka sunan Windows din da kake amfani da shi. Anan saika latsa Get Started. 

4. Allo na gaba zaka basu dalilin da yasa kake bukatat komawa tsohon naka na baya,  bayan ka zabi dalilinka saika latsa     NEXT     
Bayan sun gama gargadi da sanarwa, zasu baka dama ka koma. Sannan a kowanne lokaci zaka iya komawa Windows 10.

Sannan kana goge tsohon Windows din naka idan kana ganin wanda ka koma din yayi maka.

Wednesday, 21 February 2018

GOGE TSOHUWAR MANHAJAR WINDOWS BAYAN SABUNTA WATA ZUWA WINDOWS 10 (Delete Windows Old)
Yayin da ka sabunta manhaja zuwa window 10, windows dinka na baya zai koma cikin folder mai suna Windows Old, idan kayi Click na mazubin C zaka ganta acan kasa, amma a wannan yanayin bazata gogu ba, abinda zakayi domin ka goge folder ta Windows Old saika bi wannan matakin.

1. ka latsa "Windows Search" saika rubuta kalmar
"Cleanup",  idan ka rubuta wannan kalma saika latsa "Disk Cleanup" .

2. Saika latsa  "Clean up system files" anan duk abinda bashida amfani a PC dinka zai bayyana.
3.Ka dan jira kadan bayan ka latsa  "Clean up System files" domin yana tace abinda suke bukatar goge wa, ya yinda ya baka su. ka duba jerinsu zaka ga Windows din daya yake ma baya  "Previous Windows installation". 

4. Saika je kansa ka latsa karamar akwatin dake bayansa "Mark" sai kayi  masa alama, shi kadai. sai dai kuma idan suma sauran abubuwa da suke wurin kana bukatar ka goge su. saika latsa OK domin fara cleanup na files din.

Idan kuma kana jin cewar zaka koma amfani da tsohon windows din naka ,  downgrade from Windows 10 saika barshi, basai ka goge shi ba.

Amma ka sani koda ka barshi,  idan yakai wa'adi na kamar wata daya ko fiye, to windows 10 zai fitar da tsohon windows din naka.

Matsalar Windows.old shi ne cin wuri, tunda ba ka amfani da shi, me yiwuwa, ya ci wuri dayawa, kuma watalila computer din naka kana bukatar wannan filin da take da shi.

Thursday, 25 January 2018

DORA Windows 7 AKAN COMPUTER
Hanyar dora Windows 7, akan computer akwai hanyoyi


guda uku, zamu bisu daya bayan daya mu gabatar dasu. 

1. SAKA WINDOWS 7 TA BOOTABLE CD



Wannan hanyar itace hanyar da ake iya dora Windows 7 akan computer,  ta hanyar amfani da bootable CD, Idan kana da wannan bootable CD saika bi wadannan matakan,  domin dora Windows  akan computer dinka, Laptop,  ko Desktop, saika bi wadannan matakan. 
1. Kasa Windows 7 bootable CD acikin gidan saka CD na jikin computer dinka, idan kuma baka da shi,  ko kuma naka baya aiki, kana iya amfani da CD na waje (External CD ROM), idan kasa shi,  saika latsa My Computer domin ka tabbatar CD daka sa ya hau, idan ka tabbatar  ya hau shi kenan. 
2. Saika yi mata reboot, wato ka latsa Windows Start Menu >Switch Option sannan ka latsa Reboot. Abinda ake the bukata anan shi ne ka lura da tana tafiya reboot. 
3. Tana reboot yayinda take kokarin dawowa,  saikai sauri ka danna  F9  , ko F12, ko F7 ko ka latsa madannin C, ya danganta da yanayin tsarin boot Option na computer dinka. wanda ya latsa F7, ko F12,ko F9 akwai bukatar ya zabi CD ROM,  domin cewar yana bukatar na'urarsa ta tashi daga CD ROOM.


4. Kana zabar CD ROM zata baka bakin allo da cewar “Press any key to boot from a CD or DVD.._"

kayi sauri ka latsa ko wane irin madanni ajikin keyboard dinka kafin wannan bakin allon ya kauce, idan wannan rubutun ya kauce, saika sake mai-maita mataki na biyu dana uku.

5. Yayin daka danna kowanne irin madanni,  ko kafin ka latsa tana iya baka wannan allon,
Idan ta baka wannan allon,  saika latsa madannin "Enter" domin bukatarka ta dora Windows 7 akan pc dinka. shi wannan allon yana iya zuwa kafin mataki na hudu ma, wato  kana zabar CD ROM boot, tana iya baka wannan allon a matakinka na gaba

6. Zata baka wannan allon
 
da cewar "Windows is loading files... 
."  anan ba'a bukatar ka latsa komai. 


7. Zata baka allo na gaba,  ka zabi yaren da kake bukata Windows dinka ya sauka da shi, "Language to install"   sannan ka zabi tsarin madannai "Keyboard 


  

8. Bayan ta gama,  allo na gaba zata baka wannan
da cewar "Install now"  saika latsa "Install now" 
Bayan ka latsa "Install now" allo na gaba zata baka koren allo da cewar "Setup is copying temporary files" dan dakiku zata yi saita sake cewa "Setup is starting" tana gama wannan sai allo na gaba.

9. Bayan ya gama, allo na gaba zai baka wanda anan zaka zabi salon saukar Windows dinka, wato Upgrade zaka yi ko kuma Custom (Advanced) to anan saika zabi advance, tunda magana muke ta dora windows da CD/DVD. 

 10. Anan saika latsa yar akwatin dake kasan gargadi, da kuma yarjejiniya Accept the license agree.
11.  Anan ya danganta da yadda Windows dinka yake, wato wani CD/DVD Windows daya ne acikinsa,  wani kuma haduwar windows ne acikinsa, idan naka ya kasance yana dauke dasu kala-kala. 

 12. Bayan zabar kalar Windows din da kake bukata saika yi partition wato raba hard disk dinka gida biyu. Sannan ka zabi inda kake son ka saukar da Windows dinka.  Saika latsa Next

13. Nan take zai fara copy na files yana saukar dasu kan computer dinka, anan ba'a bukatar ka latsa komai.  Ka jira zata bukaci tayi restart,  sannan ta dawo ta karisa saukar da windows dinka, bayan ta gama da wannan matakin kana iya cire window cd dinka, ta gama saukar da shi,  saura ta gyara masa zama da tsara shi.
 14. Zaka shigar da sunan da kake son amfani dashi akan ita wannan computer,  sannan ka bata suna.
 15. Sannan zaka shigar da lambobin mallaka wadanda suke tabbatar da ingancin windows din da kasa wato product key,  lambobi ne, hade da harufa, ana iya samunsu acikin kwalin Windows CD/dvd.

16. Saika saita agogo da kwanan wata,  bayan ka zabi nahiyarka, ko kasarka. 

 I
17. Saika zabi recommending settings a allo na gaba, aikinka ya kammala.  Saika more lokaci da windows 7 dinka.