Idan kana bukatar cire Password ko Pattern ko PIN ajikin wayarka tecno P3 saika bi wadannan matakan.
1. Ka kashe wayar taka wato ita wannan tecno P3 (Switch it off)
2.
Ka danne wurin karin sauti (Volume Up) sannan da makunna (Switch On/Off) atare guda biyun, karka daga su, har tsawon kamar dakika 10, zata baka allo baki wato "recovery Menu"
Ka danne wurin karin sauti (Volume Up) sannan da makunna (Switch On/Off) atare guda biyun, karka daga su, har tsawon kamar dakika 10, zata baka allo baki wato "recovery Menu"
3. Saika daga wadannan madannai, idan batayi ba, ka sake cire batir ka mayar, saika bi mataki na 1 dana 2.
4.Bayan ta baka wannan allo saika yi amfani da Volume Up da Volume Down domin zabin inda kake bukata, saika latsa ""DATA WIPE/FACTORY RESET"
5. Saika yi amfani da Power On/Off amatsayin madannin "OK"
Idan akwai password, pattern ko PIN zai fita nan take,.
Kuskure matakin ko zabar wani abu daban, ka iya jefa wayarka wani hali, bamu dauki nauyin lalacewar wayarka ba.
GARGADI
Yin factory reset zai goge duk abinda
yake kan wayarka, PIN, Password, Pattern, Lambobin kan waya, Wakokin
kan waya, Hotunan Kan waya, da app ko Video. ka tabbata ka dauki abinda kake
so kafin fara aikin. .
|
1 comments:
inada tambaya
Post a Comment