Monday, 5 February 2018

MINENE ROOTING KUMA MIYE AMFANINSA A ANDROID DA KUMA RASHIN AMFANINSA?

Duk da nasan mafiya yawan masu amfani da android sun riga sunsan kome ake nufi da root sannan kuma sun iya root din to duk da hakande nasan wasu haryanxu basu gane mi wannan kalmar take nufiba
.
To Alhamdulillah a wannan shafi zakusan bayani akan root
.
Rooting samun dama ce akan operating system din wayar ka, domin sarrafa ta yadda kake so, idan kai masanin computer ne rooting Kaman samun dama ne akan windows dinka ko administrator rights, misali a cafΓ© idan zakayi wani abu se ace "you do not have permission to do that" sabida administrator din ya iyakance maka abunda zaka iya yi, ko kuma in kana da laptop kai amatsayin me computer zaka iya komai amma me amfani da "guest account" bashi iyawa…
rooting kenan zata baka daman yin komai da administrator yake yi, idan kai masanin wayar symbian ne Kaman yadda amfani da x-plore take nuna maka komai nakan folders din ka haka android zata koma idan anyi rooting, koda kuma ba’ayi rooting ba zaka iya installing application me buqatar rooting sede bazatayi aiki ba, zata rubuta root access denied ko tace no root privileges…
Rooting tana bada daman shiga lungu da saqon wayar ka, akwai restrictions ada yawa a wayoyin android amma sanadiyar rooting se kaga ka samu dama ka wuce restrictions din..
.
Kena a taqaici yin haka a Android kaman Hacking ne a Symbian, kunsan itama symbian ana mata hack domin samun dama nayin wasu abubuwa akanta cikin sauki wanda rashin yi mata wannan hack din xai iya hanaka yin wani abun sannan kuma Kaman jailbreaking ne a iOS (iPhone, da iPad)…
kuma Android kadai akeyiwa rooting
.
MENE NE AMFANIN ROOTING? KUMA DOLE NE SE NAYI ROOTING NA WAYANA NA ANDROI?
.
A’a ba dole bane kayi rooting wayar ka ta android idan kai ba irin wanda baya riqe waya dan fashion bane sai dan sirrikan da ke wayar tare da karantar ita kanta wayar ta inda duk wata matsala zaka iya sanin dalilin ta… Idan burin ka shine kaga ka riqe wayan kana kira, koka hau 2go ko fb, ko kayi chatting a whatsapp, ko kallon videos da daukan hoto to baka da buqatan rootin…. Amma idan kai burin ka ka cika wayar da application ne kuma kai ma,abocin browsing ne da son ganin kana upgrading version din android dinka Kaman yadda masu bb sukeyi, ko ka canza ma wayar fasali ta yadda wani can me irin wayar ka zeyi mamakin ganin naka domin banbancin su a application to kana buqatar rooting…
.
AMFANIN ROOTING SUNA NAN KAMAN HAKA….:
.
1. Zaka samu daman installing HD game masu girman gaske, kuma ya hau wayar ka koda kuwa ba HD bace.
2. Zaka samu daman installing applications kowani iri, Kaman file explores masu bude zip files harda ganin qoqon cikin wayar, da applications Kaman anti virus wanda ze kare ka daga virus gurin browsing ko ta Bluetooth,
3. Rooting ze baka daman using VPN service wanda shi aikin VPN shine ya boye ip address dinka ta yadda idan kana Nigeria kana browsing, ze riqa nunawa Kaman kana wani qasa ne can waje, kuma idan akwai restrictions misali Kaman MTN to VPN din ze hana mtn blocking dinka… (Har Free Browsing zaka iya yi idan kayi rooting)
4. Rooting zai baka daman qara RAM din wayar ka, idan kai masanin computer ne zaka fahimci mene ne RAM, shi, RAM wani Hardware ne wanda ke taimaka wa gurin saurin sarrafa abu a na’urar ka, saurin wayar ka ta Android is determined by the availability of your RAM, wasu RAM din wayar su rabin 1gig
.
Wannan shine dan takaitaccen bayani akan root
.
Insha Allah zamuyi bayanin yadda ake root din anan gaba

0 comments: