Google Search Engine
Yadda muka saba bincike da
injin bincike na google, mukansha wahala
ko kuma samuwar amsa barkatai da sassa na web da suke a duniyar intanet, hakan yakan samu rudani wejen
tantace wanne gaskiyar abinda muke nema, ga wannan atakaice kan yadda zakayi
bincike da google search engine
BINCIKEN ZAUREN SADA
ZUMUNTA (SOCIAL MEDIA)
Idan kana bukatar binciken
wani zauren sada zumunta, ko kuma wata magana da aka tattaunata a wannan zaure
da kake bincike saika rubuta maganar, amma yayin da zaka sa sunan zauren ana
bukatar kasa alamar @ misali: @twitter, ko @instagram.
SANIN KUDIN ABU TA HANYAR Google SEARCH (PRICE)
Kana bukatar siyan abu, amma
kudinka kana tunanin wannan abun kudinsa yana da yawa, ko kuma kana bukatar
wannan abu na dala dari biyar, abinda
zakayi anan shi ne ka ziyarci Google search saika shigar da sunan abinda kake bukata
sannan ka shigar da alamar dala ($) misali
Samsung mobile $500, kana turawa
zasu kawo maka hotunan samsung masu wannan ko kuma wayar da kake bukata kana
son ta wani adadi kamar kana son waya Samsung daga $25 zuwa $100, saika shigar
a Google misali Samsung $25..$100, anan iya wayoyin Samsung da suke tsakanin wannan farashi
zasu kawo maka, saika zabi kala.
BINCIKE DA HASHTAG
Kasa alamar # yayinda kake
bincike da google anasa alamar # aduk farkon kalmar da zaka binciko
misali: #duniyarwaya, #bbchausa
BANDA WANNAN KALMAR ACIKIN BINCIKENKA
Ana sa wannnan alamar ta
collon (-) afarkon kalmar da baka
bukatar ta abincikenka misali: duniyar waya -computer, anan zasu baka bayani
akan duniyar waya, amma duk inda computer yazo bazasu kawo maka post din ba, ko
misali: speed vihycles -car, zasu
kawo sauran abun hawa amma bazasu kawo mota ba.
BINCIKE AKAN ABINDA BAKA SANI BA
Tayiwu akwai abinda kake da
karin bayani akansa, ana amfani da alamar * acikin kalma ko jimla domin samun
cikaken bayani tare da amsa mai inganci misali: "Largest * in the world"
HAKIKANIN ABINDA KAKE NEMA
Domin samun hakikanin abinda
kake nema saika yimfani da quotation mark ( ") yayin gudanar da bincike, misali: "labarin wasanni bbc hausa" saka rubutunka tsakanin
wadanna alama, shi yake nuni wannan abin kadai kake da bayan
KAYYADE IYAKAR ABUN DA KAKE BUKATA (SEARCH WITHIN A
RANGE OF NUMBERS)
Kasa alamar .. Tsakanin
abinda kake bukata misali kana bukatar waya kirar LG wacce kudinta ya fara
daga dollar 100 zuwa dollar 200,
abinda zakayi shi ne
misali: LG mobile $100..$200 zasu baka hoton waya ne masu wannan farashin
zasu baka ta kasa da farashin ba, sannan ba zasu baka ta sama da shi ba.
HADUWAR BINCIKE
Misali idan zaka binciko
kalmomi biyu, ko wasu abubuwa
mabam-banta saikayi amfani da Kalmar ( Or) tsakaninsu misali Waya
Or Computer.
BINCIKEN SITE
Yin amfani da kalmar 'site' tana tabbatar maka hakikanin
website din da kake bukata, ana sata
afarkon rubutu misali: site:duniyarcomputer.com ko
site:duniyarwaya.com wannan zai baka hakikanin wadannan gidaje da ka
bukata.
SEARCH FOR RELATED SITES
Rubuta kalmar "related" a farkon web
address misali: related:bbchausa.com
SAMUN BAYANAI AKAN WANI GIDAN (SITE
INFO)
Kasa kalmar "info" afarkon shigar da
sunan web address misali: info:facebook.com
0 comments:
Post a Comment