Wannan waya mai suna Asha, tayi yawa a hannun mutane, kuma
suna daukan Asha amatsayin duk abinda wata babbar waya zatayi Asha ma zata yi,
to wannan ba gaskiya bane, kuma Nokia Asha Java ce, bazaka hada ta da Symbian.
Nokia Asha tana da yawa kala-kala ce takai kala biyar, misali ka dauki Nokia
Asha 200 zaka ga akwai bambanci idan ka hada guda biyu ko uku zaka ga akwai
abinda yake a wannan babu a wannan, zaka gane wannan matsala ne idan ka shiga
cikin Settings na wayanka saika zabi ''Configuration'' ka bude shi kamar na
waya biyu zaka ga bambancin dake ciki. Wata tana bada damar mutum ya kirkiri
''personal configuration'' wata kuma bata da shi saidai ''Access point''.
MATSALAR DOWNLOAD A NOKIA ASHA
Idan kana da Nokia Asha
tana baka matsala wajen download wato tana nuna maka wasu abubuwa kamar haka, > Check connection > Package data
failed > Failed to connect to the internet > Operation failed >
Connection server failed ko dai bata maka download duka, to kabi wadannan matakan
na kasa.
Internet Settings
Idan kana samun matsala da ita
saika duba setting na wayanka, ko
kuma ka tura sakon ‘settings’ zuwa
ga kamfanin layinka, kamar haka:
> Idan kana amfani da MTN akan Asha naka danna *123*1*4# zaka samu setting na browsing
mai kyau sai kayi save nasa. Ko ka
tura “Settings’’ zuwa 3888.
> Idan kuma kana amfani da 9mobile/etisalat saika tura ''SETTINGS'' zuwa 790, zasu turo maka
sai kayi Save nasa.
> Idan kana amfani da glo saika tura misali ''All Nokia Asha 200'' zuwa 1234, zasu
turo maka saika danna reply da ''YES''
zuwa 4321.
> Idan kana amfani da Airtel
saika tura misali ''internet Nokia Asha
200'' zuwa 232. Zasu turo maka
sai kayi save.
Bayan ka tura da layin da kake amfani kuma
sun turo maka harma kayi Save nasa,
to saika bi wadannan matakan dan bashi damar yin download, Bude ''Menu > Settings > Configuration''
Idan taka mai ''Access point” ce
kadai saika danna shi ka zabi sunan kamfanin layinka misali ''MTN'' saika danna save. Sai Internet access saika danna Apply
saika dawo da baya ka fara download ka gani. Idan kuma taka tana da Configuration ne saika danna save. sannan Access point ka zabi na sunan layinka saika danna Apply ka dawo da baya wurin yin browse
ka gani zata fara yi maka download
0 comments:
Post a Comment