Thursday 15 February 2018

YADDA AKE SETA MTN NG A BROWSING


Idan kana amfani da layin MTN sannan kuma
kana son dora shi akan intanet, wato kayi
browsing da shi, to ga yadda zakayi.
1. Idan kana amfani da waya Original saika shiga
message ka tura kalmar: ''Settings'' zuwa 3888.
2. Idan kuma wancan yayi maka tsauri, sannan
kuma kana amfani da waya Orinal, saika danna
*123*1*4#. Zaka samu setin browse mai kyau
akan wayarka cikin sauki.
Sannan kuma idan kana amfani da China mobile,
ko kuma Original ce, amma bata karbar wancan
wato misalinsu HTC, GiONEE, Huwaei BB,
Android phone, ko iPhone da sauran wayoyi
wadanda basa karbar daga kamfani kai tsaye,
saisu yi amfani da wannan na kasa.
Ko kuma wayanka Nokia ce, amma bata bude
operamini ko sauran browsers, wato batada
Access point kenan, saikayi amfani da wannan
na kasan.
1. Ka kirkiri sabon setting cikin Data account ko
Connectivity ko personal Configuration ga mai
Nokia.

2. Saika shigar da wadannan abubuwan cikin
setin naka, wato ka cike wuraren da aka baka

Account Name:           MTN
Homepage:          http://wap.mtnonline.com/
Username:         web
Password:          web
Access Point (APN):          web.gprs.mtnnigeria.net
IP/Proxy Address:         010.199.212.002
Port:          8080

0 comments: