Thursday, 8 February 2018

KANKARE TECNO C8 (FACTORY RESET TECNO CAMON C8)

Kankare tecno C8, yakan kasance kamar flashing,  domin zai cire password, PIN ko Pattern dakasa akan wayarka.

1. Ka kashe wayar, ka tabbata tana da Chaji.
2. Ka danne wurin karin sauti da makunna (Volume Up + Power
key) alokaci daya na dan dakikoki.
3. Idan ka danne mataki na biyu,  zai baka allo na gaba,  wato tambarin android wannan koren. 
4. Idan wannan hoton na android ya fito saika latsa makunna zai baka allo na gaba. saika latsa Volume up sau daya. 
5. Yi amfani da makaren Sauti (Volume buttons)  ka zabi  " wipe data/factory
reset " saika latsa Power button
domin zabi. 
6. Allo na gaba saika latsa "Yes" 
 
7. Ka jira ta gama saita dawo allo na biyu, anan saika zabi " reboot System
now " 
Ka samu nasarar kankare wayarka tecno Camon C8.


GARGADI
Yin factory reset zai goge duk abinda yake kan wayarka,  PIN, Password, Pattern, Lambobin kan waya, Wakokin kan waya, Hotunan Kan waya, da app ko Video. ka tabbata ka dauki abinda kake so kafin fara aikin. .

Related Posts:

0 comments: