Shi wannan salon yana da muhimmanci ga wanda yake kasuwanci ko yake da kima awurin abokan mu'amala, wato akan samu masu kutse cikin account din mutum kai tsaye saboda sun san sunanka, da password dinka, amma idan kana da wannan tsarin kenan koda mutum yasan bayananka bashi da damar shiga akan wayarsa, dole saika sani, wato bai isa ya yi maka kutse har ya bukaci kudi awurin wasu mutanenka ba.
Shi salon tsaro na Backup Code yana yiwuwa ne idan ka kunna Two-Factor Authentication kuma duka tsari biyun basa aiki saika shigar da lambar wayarka. Idan baka shigar da lambar wayarka ba, bazaka ci wannan moriya ba, harsai ka shigar da lambar wayarka.
Domin samun jerin Backup code da suke da alaka da account dinka na Instagram, ko kuma ka mallaki Backup code din account dinka saika bi wadannan matakan
1. Kaje "Profile" dinka na Instagram idan nau'in su iPhone ne da kai saika latsa

Idan kuma android ce dakai saika duba saman allon wayarka daga dama ka latsa

2. Saika je kasa ka latsa "Two-Factor Authentication "
3.Saika latsa Get Backup Codes
Yayinda ka mallaki Backup code dinka, saika adana su, ko ka dauki hotonsu kadai ajiyesu awuri na musamman, amma hakan bazai yiwuba sai ka bi takan account dinka, sannan zaka iya samun naka.
CHANZA BACKUP CODE BAYAN KA MALLAKA
Yayinda ka mallaki Backup code dinka, sau kuma kake ganin cewar angane naka, ko kuma kana bukatar canza su, saboda wanj dalili naka saika bi wannan matakin
1. Kaje "Profile" dinka na Instagram idan nau'in su iPhone ne da kai saika latsa

Idan kuma android ce dakai saika duba saman allon wayarka daga dama ka latsa

2. Saika je kasa ka latsa "Two-Factor Authentication"
3.Saika latsa Get Backup Codes
4. Get new codes
Anan insha Allah zakayi maganin barayi, macuta wadanda suke kwace account na mutum ko bara zana.
0 comments:
Post a Comment