Sunday 25 March 2018

KARAWA INSTAGRAM TSARO DA SALON two-factor authentication

Shi two-factor authentication salo ne da yake kara tsaro bangaren Instagram ta yadda babu wanda zai bude shafin na instagram ba tare da ka sani, wato da zarar wani zaiyi kokarin hawa asusun ka na muhawara da zumunci na instagram zaka sani nan take.

Aduk Lokacin da two-factor authentication, yake a kunne wato idan ka saita shi da account dinka na instagram, to duk lokacin da ka shiga Instagram daga na'urar da ba a sani ba za'a tambayeka ka shigar da lambar tsaro ta SMS, wato akwai lambobin tsaro da za'a turo zuwa layinka, wanda matukar ba'a shigar da suba,  to instagram dinka bazai budu akan wannan waya ko computer ba, Sannan dole ka shigar da Username dinka da password, domin seta "two-factor authentication" saika bi wadannan matakan:

1. Kaje "Profile" dinka na Instagram idan nau'in su iPhone ne da kai saika latsa
Idan kuma android ce dakai saika duba saman allon wayarka daga dama ka latsa
2. Saika je kasa ka latsa " Two-Factor Authentication" 
3. Saika latsa  zai tambayeka lambobinka na sirri, saika shigar da su, ta haka ne zai fara aikinsa. 
4. Idan account dinka na Instagram bada lambar waya ka bude shi ba, anan zai tambayeka ka shigar da lambar wayarka, idan kuma bakayi mata Comfirm ba,  to anan zai turo maka da lambobi cikin layinka, idan ka shigar dasu saika latsa "NEXT" 

Idan  Two-Factor Authentication ya fara aiki,  zaka mallaki Back-Up Codes wato lambobi ne da zaka gyara  matsalar account din naka koda basu turo maka "Code" cikin layinka ba.

Idan baka bukatar  Two-Factor Authentication yaci gaba da aikinsa saika bi mataki na sama wato daga mataki na 1 zuwa na 3. 

Idan Two-Factor Authentication yana kunne zaka ganshi launin alama 

Idan kumaTwo-Factor Authentication yana kashe (Off) zaka ganshi yana launin fari 

0 comments: