Sunday, 18 February 2018

DAN DUBA A COMPUTER
Wani sabon Malamin duba ne na zamani, mai duba har hanji amma yana amfani ne da computer wajen gudanar da aikinsa na duba.

Gogan ana nan wata rana wasu,  suka siyo bijimi akasuwa, amma a daren da aka kawoshi, sai wannan bijimi ya bata, sai akace aje wurin malam mai duba har hanji. zuwa wurinsa keda wuya ya shiga na ura ya bincika, sai yace afita neman wannan bijimi ta yamma da gari, baiyi nisa ba, zasu sameshi.
aka ninka yamma akai ta yawon nema amma ba'a gani ba,  har aka kwana daya,  sai akace ayi gabas tunda anbi kwantancensa,  ba'a dace ba, suna yin gabas saiga su sun samo bijimi, sai gogan ya kada baki yace,  aidama nace a danyi gabas sannan ayi yamma. 
KIRAN WAYA NE
Wani saurayi ne dan kwalisa awurin mata,  amma ya kware wajen ciye-ciyen abinci,  rannan gogan ya tsaya da wata yarinya suna zance, gogan tusa ta matseshi, irin wacce bazata rukuba, kafin ya ankara tuni ta fito Bir-bibir-birrrrrrrrr, sai yan mata ta ankara, sai tace meye haka, gogan yace "Sharesu kawai, wani ne yake tamin filashin" , sai tace haba tusa fa kayi, sai gogan ya fusata, anyi din ke bakya yi ne.

SAURA MIRFIN WAYAR
Wani gaye ne dan karfin hali, ya kunzige ya sayi waya mai tsada, aranar daya siyeta, ya tama zai buga birni da ita,  can yana zaune sai turoso (toilet)  ya matseshi, nan take ya nufi gidan wanka, shigarsa ke da wuya zai tsugunna, sai wayar tana gaban aljihunsa, ta taho, nan ta bigi bakin masai din gidan wanka, waya ta fada cikin masai, batir din shima ya bita, saiya rage murfin wayar ne ya fadi can gefe,  gogan nan take turoso ya fece,  me kake ganin ya kamata yayi da murfin wayar daya rage masa? 

Thursday, 8 February 2018

BAZAZZAGI DA WATA BUDURWA A KANO

Wani Bazazzagi ne a Kano, yana jin cewar shi gaye ne agarinsu yazo Kano, sai yaga waya yadinya hadaddaiya, kunsan Bazazzagi da mace, nan dai ya tare ta yana rawar jiki, zance ya fada yace ta ba lambar wayarta nan ta karanto masa,  amma shi gogan ana tambayarsa lambar wayarsa bai sani ba, kuma ya rasa inda zai gano ta, nan take ya ciro layin wayar tasa ya mika mata cewar intaje gida,  tasa layin a waya ta dauki lambar idan tasa kati, sannan ta kirashi yazo ya karba. nan ta kyal-kyale da dariya, tace miye lambar layin naka,  yace mata Airtel ne tace masa ka latsa *1# ko *9# zaka ga lambar wayar.

Tuesday, 16 January 2018

YA ZACI WAYARSA SABULUCE
Akwai wani mutum yaje gidan wanka zaiyi wankin kayansa,  dama ya siyo sabulunsa yana aljihunsa, sannan wayarsa itama tana daya aljihun nasa,  gogan yana zuwa zai yi wanki,  ya jika kayan nasa,  kawai saiya sa hannu a aljihunsa,  zai dauko sabulu,  ashe aljihun da waya take nan yakai gannu,  gogan ya dauko waya,  ya dinga goga ta ajikin kayansa,  ya dinga sabata,  amma shi baiga kumfa ba,  ya dulmiya waya can kasan kaya wai irin sabulun nan ya jika, yasake dagota,  yaci gaba da gurzar kaya, amma baiga sabulu yayi kumfa ba,  ya duba sabulu sai yaga ashe wayarsa ce yake ta tsomata aruwa yana gurza kaya.