Saturday, 11 March 2023
Sunday, 27 November 2022
Wannan sune lambobin sirri na waya, keypad, musamman tecno ko Itel,sannan suna aiki akan wasu wayoyin, amma idan kayi amfani dashi a wayarka baiyi ba, kayi comment da sunan wayarka saimu baka lambobin naka wayar.
PIN ɗin da duk wata waya keypad take zuwa da ɗaya daga cikin waɗannan
AIKIN LAMBOBIN SIRRI | LAMBAR SIRRI | |
01 | Lambar sirri da duk keypad take zuwa dashi | 1122, 3344, 1234, 12345, 0000, |
02 | Gyara matsalar cikinta (Engineer mode) | *#110*01# |
03 | Quick test | *#87# |
04 | Goge kan wayarka duka | *#0*# |
05 | Enable COM port | *#110*01# |
06 | LCD contrast | *#369# |
07 | Software version | *#900# ko *#800# |
08 | Yaren da waya tazo dashi | *#0000# sai a kira |
09 | Juya yare zuwa turanci | *#0044# sai akira |
10 | Set English language (new firmware) | *#001# sai a kira |
11 | Seta Voicemail | Lamba 1 za'a danne |
12 | Goge kan waya duka | *#12345# |
𝘽𝙖𝙢𝙖 𝙨𝙖𝙠𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙘𝙤𝙙𝙚, 𝙙𝙖𝙣 𝙬𝙖𝙣𝙞 𝙮𝙖 𝙘𝙪𝙩𝙖𝙧 𝙙𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙞, 𝙢𝙪𝙣𝙖 𝙠𝙖𝙬𝙤 𝙨𝙪𝙣𝙚, 𝙙𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙮𝙖ɗ𝙖 𝙨𝙖𝙪ƙ𝙖 ƙ𝙚ƙƙ𝙚𝙣 𝙄𝙡𝙞𝙢𝙞 𝙯𝙪𝙬𝙖 𝙜𝙖 𝙖𝙡'𝙪𝙢𝙢𝙖𝙧 𝙢𝙪 𝙩𝙖 𝙃𝘼𝙐𝙎𝘼.
𝘿𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖𝙧 𝙒𝙖𝙮𝙖 𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙜𝙤𝙮𝙤𝙣 𝙗𝙖𝙮𝙖𝙣 𝙘𝙞𝙣 𝙯𝙖𝙧𝙖𝙛𝙞𝙣 𝙬𝙖𝙣𝙞 𝙠𝙤 𝙢𝙪𝙜𝙪𝙣𝙩𝙖 𝙖𝙠𝙖𝙣 𝙖𝙢𝙛𝙖𝙣𝙞 𝙙𝙖 𝙖𝙗𝙞𝙣𝙙𝙖 𝙢𝙪𝙠𝙖𝙮𝙞 𝙥𝙤𝙨𝙩. 𝙢𝙪𝙣𝙖 𝙢𝙖𝙧𝙝𝙖𝙗𝙪𝙣 𝙙𝙖 𝙢𝙖𝙨𝙪 𝙗𝙖𝙢𝙪 𝙨𝙝𝙖𝙬𝙖𝙧𝙖 𝙠𝙖𝙞 𝙩𝙨𝙖𝙮𝙚.
Thursday, 17 November 2022
Monday, 21 December 2020
YADDA ZAKA HAƊA LAYINKA NA MTN DA KATIN ƊANKASA
Kamar yadda sanarwa ta fita daga Gwamnatin tarayya, ta ma'aikatar sadarwa, "Nigerian Communication Commission" (NCC) cewar akwai bukatar duk ɗan Nigeria, daya tabbatar ya hada layin wayar sa da Katin sa na ɗan kasa, domin tabbatar da tsaro, sannan aka bada ƙaramin wa'adi, kan cewar duk wanda bai aiwatar ba, zai iya jin layinsa akulle, sati biyu akaba duk ɗan kasa, daya tabbata yayi wannan hadin.
Ɗaya daga cikin gudun mawar da kamfanin layi suka taimaka domin rage cunkoso shi ne kowa zai iyayi daga gida basai ka ziyarci ofishinsu ba, matukar kana da katin ɗankasa, wannan shi ne na MTN
1. Ka tabbata layinka MTN ne.
2. Ka tabbata kana da katin Ɗan kasa, kuma yana hannunka
3. Akan layinka na MTN saika danna *785# ko *789#.
Zasu baka allo, cewar ka shigar da lambar mallakar katin dan kasa "NIN Serial Number) guda goma sha daya ce.
Wannan shi ne hanya mafi sauki da zaka tseratar da layinka daga kullewa, kuma zuwa 30 ga watan 12, na wannan shekarar da muke ciki 2020. Ka gaggauta yi domin tsira da layinka.
Yana iya yiwuwa, kana da katin ɗan kasa, ka rasa inda ka sa shi, wani ma nasa ya ɓata, to ga yadda zaka yi ka samu Serial Number ɗinsa, cikin sauki basai ka sake yin wani ba, domin haɗa shi da lambar wayarka.
1. Ka tabbata kaine ka yi rijistar sa.
2. Ka tabbata layinka daka yi rijistar katinka na dan kasa yana aiki, wato alokacin rijista anbuƙaci lambar wayarka, to ita wannan lamba daka bayar ka tabbata tana aiki yanzu, kuma tana kusa da dakai.
Koda bata wurinka, matukar kana kiranta zaka iya rokon arziki ya taimakeka, ya duba maka,
3. Idan layin yana wurinka ka danna *346# nan take zasu turo maka da lambobin da ake bukata a wannan lokaci.
Idan layin naka ya ɓata to bazai yi da sabon layinka ba, matukar bada shi kayi katin Ɗan ƙasa ba.
Monday, 26 March 2018
Misali mu dauki Mixi account, shi wannan shima dandalin sada zumunta ne amma na yankin Japan ne kadai, kenan kaga wanda baya yankin Japan to bazai mallaki shi wannan account na Mixi ba, saboda wayarka ce ta ce musu ba'a yankinsu kake ba, wato anan setin da wayarka take dauke dashi shi ne, setin agogo bana yankinsu bane, sannan shi kansa yankin ka ba nasu bane (Region) sannan yarenka ba nasu bane.
Idan kana bukatar amfani da irin wadannan zauruka saika bi wannan matakin
1. Kaje phone's Settings saika latsa General > International > Region Format. Saika zabi Japanese (Japan)
Kana maida shi, shikenan kaje ka budeshi nan take zai bude, kuma koda kana bukatar hadashi da wasu zaurukan idan kaje setin dinsu zaka ganshi awurin, misali kamar kana bukatar ka hada shi da Instagramzaka ganshi.
Abu na biyu shi ne kamar weibo shima yana yine a yankin kasar China, idan ka duba Vivo, Oppo, Lenovo ko wasu daga GiONEE zaka samu wadannan zauruka acikinsu, tunda dama wayoyin wasu daga cikinsu na kasar China ne da nahiyarsu. Saika bi wadannan matakan shima
1. Kaje phone's Settings saika taba General > Language & Region > awurin da akasa Region saika zabi Chinese ko dai wata kasar da take nahiyar (China, Taiwan da sauransu) saika latsa DONE, idan ka dawo ka bude shi zaiyi aiki nan take, ko kuma idan kana bukatar hadashi da zauren sada zumunta, kamar instagram.
Duka zaurukan sada zumunta Facebook, Twitter ko Instagram ba kowanne yake da sauki kamarsu ba, saboda su duniya ce. Sai wasu kasashen da basa ta'ammali dasu ko yi musu iyaka.
To bisa ga yadda ake yin post, wani yafi Bukatar yayi post a Instagram sannan yana da account da wani zauren amma sai kaga acan ba'a tattaunawa dashi. Wannan rubutu zai fahimtar damu yadda zaka hada Instagram dinka da wasu zaurukan sada zumunta, inda duk lokaxin da kayi post a daya daga cikin zaurukan, mabiyanka na kowanne zaure zasu ga abinda kayi post hoto, bidiyo, ko rubutu.
Misali idan ka hada Instagram dinka da twitter to idan kayi rubutu a Instagram to abokanka na Twitter zasu gani, hakan idan kayi a twitter, na instagram dinka zasu gani.
Idan kana bukatar hada instagram dinka da twitter ko wani zauren sada zumunta, saika tabbatar kana da account da su, sannan saika bi wadannan matakan:-
1. Ka bude Instagram dinka, a profile dinka saika taba
2. Idan iPhone ce da kai saika tabaIdan kuma Android ce taba
3. Saika taba Linked Accounts, sannan ka taba zauren sada zumunta da kake bukatar ka hadesu "social network to log in and link the accounts"
Kana hadesu shi kenan, aduk lokacin da ka dauki hoto, bidiyo ko rubutu daga instagram zai bayyana a wadancan shafukan. Koda kuwa zauren sada zumuntar babushi a kasarka, misali akwai dandalin muhawara na wasu kasashe kadai,kamar irinsu China zaka samu suna da zaurukan sada zumunta na yankunansu.
Sunday, 25 March 2018
Shi wannan salon yana da muhimmanci ga wanda yake kasuwanci ko yake da kima awurin abokan mu'amala, wato akan samu masu kutse cikin account din mutum kai tsaye saboda sun san sunanka, da password dinka, amma idan kana da wannan tsarin kenan koda mutum yasan bayananka bashi da damar shiga akan wayarsa, dole saika sani, wato bai isa ya yi maka kutse har ya bukaci kudi awurin wasu mutanenka ba.
Shi salon tsaro na Backup Code yana yiwuwa ne idan ka kunna Two-Factor Authentication kuma duka tsari biyun basa aiki saika shigar da lambar wayarka. Idan baka shigar da lambar wayarka ba, bazaka ci wannan moriya ba, harsai ka shigar da lambar wayarka.
Domin samun jerin Backup code da suke da alaka da account dinka na Instagram, ko kuma ka mallaki Backup code din account dinka saika bi wadannan matakan
1. Kaje "Profile" dinka na Instagram idan nau'in su iPhone ne da kai saika latsa
Idan kuma android ce dakai saika duba saman allon wayarka daga dama ka latsa
2. Saika je kasa ka latsa "Two-Factor Authentication "
3.Saika latsa Get Backup Codes
Yayinda ka mallaki Backup code dinka, saika adana su, ko ka dauki hotonsu kadai ajiyesu awuri na musamman, amma hakan bazai yiwuba sai ka bi takan account dinka, sannan zaka iya samun naka.
CHANZA BACKUP CODE BAYAN KA MALLAKA
1. Kaje "Profile" dinka na Instagram idan nau'in su iPhone ne da kai saika latsa
Idan kuma android ce dakai saika duba saman allon wayarka daga dama ka latsa
2. Saika je kasa ka latsa "Two-Factor Authentication"
3.Saika latsa Get Backup Codes
4. Get new codes
Anan insha Allah zakayi maganin barayi, macuta wadanda suke kwace account na mutum ko bara zana.
Aduk Lokacin da two-factor authentication, yake a kunne wato idan ka saita shi da account dinka na instagram, to duk lokacin da ka shiga Instagram daga na'urar da ba a sani ba za'a tambayeka ka shigar da lambar tsaro ta SMS, wato akwai lambobin tsaro da za'a turo zuwa layinka, wanda matukar ba'a shigar da suba, to instagram dinka bazai budu akan wannan waya ko computer ba, Sannan dole ka shigar da Username dinka da password, domin seta "two-factor authentication" saika bi wadannan matakan:
1. Kaje "Profile" dinka na Instagram idan nau'in su iPhone ne da kai saika latsa
Idan kuma android ce dakai saika duba saman allon wayarka daga dama ka latsa
2. Saika je kasa ka latsa " Two-Factor Authentication"
3. Saika latsa zai tambayeka lambobinka na sirri, saika shigar da su, ta haka ne zai fara aikinsa.
4. Idan account dinka na Instagram bada lambar waya ka bude shi ba, anan zai tambayeka ka shigar da lambar wayarka, idan kuma bakayi mata Comfirm ba, to anan zai turo maka da lambobi cikin layinka, idan ka shigar dasu saika latsa "NEXT"
Idan Two-Factor Authentication ya fara aiki, zaka mallaki Back-Up Codes wato lambobi ne da zaka gyara matsalar account din naka koda basu turo maka "Code" cikin layinka ba.
Idan baka bukatar Two-Factor Authentication yaci gaba da aikinsa saika bi mataki na sama wato daga mataki na 1 zuwa na 3.
Idan Two-Factor Authentication yana kunne zaka ganshi launin alama
Idan kumaTwo-Factor Authentication yana kashe (Off) zaka ganshi yana launin fari
Thursday, 22 March 2018
Kasani:- Duk matakin da ake dauka yana yiwuwa ne ka seta tsarin kafin a dauketa, bayan an dauke ta,idan kayi tunanin ka saita ba zaiyi ba, bazai gano maka ba matukar kafin ta bata baka saita shi ba.
Da wannan application zai baka dama ka sarrafa wayarka idan bata hannunka, wato idan ka tabbatar an dauke ta, akwai abubuwan da zai iyayi da taimakonka.
Sannan shi wannan Easy finder yana aiki akan kowacce waya, matukar tana da Java, ga wadanda suke da Java phones suna iya dauko NQ Anti-Virus, ko Netqin Anti-Virus duka suna dauke da wannan tsari na easy finder, haka wanda yake da Symbian shima yana iya dauko NQ Anti-Virus, ko Netqin Anti-Virus.
I. Idan wayar taka ta, bata ko kuma wani naka ya dauki wayar ana cire layinka zai sanar da kai cewar an canza layin dake cikin wayarka, ka tuntuba kaji ko sacewa akayi, wannan sakon da zai turo, zai turo ne alamba ta musamman kamar lambar yayanka ko wani daka sa lambar sa domin ya sanar dashi abu ya faru awayarka.
II. Kana iya adana kayan cikin wayar ta hanyar tura sako zuwa wannan sabuwar lamba da take kan wannan waya, nan take zai kwashe maka kayan ya adana maka su a emai dinka da kayi rijista dashi.
III. Kana iya kulle ta nan take.
IV. Sannan shi easy finder zaici gaba da turo maka hoton wurin da wayar take duk bayan minti biyu, kana iya seta shi kasa da haka, zaici gaba da turo maka taswirar wurin (area map)
Domin ka saita shi akan wayarka kabi wadannan matakan
1. wanda yake da Android saika je Playstore ka dauko
Ga wanda yake da Windows Phone saika je Market place/Store na Windows dinka ko kuma latsa nan
Wanda yake da Java phone saika latsa nan domin ka dauko na wayarka.
2. Ka saukar da shi (install) sannan ka budeshi.
3. Zai baka allo na farko ka jira zai baka allo na gaba
4. A wannan allo zai bayyana maka, cewar karka damu idan wayarka ta bata, zai nuna maka aikin da zai maka akan wayarka bayan ta bata ko ansace. Anan saika latsa Get Started.
5. Zai zabin aikinsa yana da tsari na kyauta, sannan yana da tsari na biyan kudi, kuma N100 zai dauka daga kudin cikin wayarka, domin samun aikinsa na (Premium) Idan ka amince su dauki N100 awayarka saika latsa Yes idan kuma na kyauta kake bukata saika latsa No thanks
6. Allo na gaba saika taba tsakiyarsa wato inda hoton waya yake, nan zaka taba, wuri mai launin kala dake tsakiyar taswira nan zaka taba.
7. A wannan matakin, zaifi kyau kayi rijista da wannan application domin cin wata gajiyar dole saikayi rijista dashi. Saika latsa Sign In domin rijista, domin sai kayi rijista ne Easy finder zai iya turo maka taswjirar hoton wurin da wayarka take (area map) sannan sai kayi rijista dashi zai iya baka dama kayi Backup na kayan cikin wayarka, sannan saikayi rijista zaka iya shiga shafinsu na intanet domin bincikar inda wayarka take, sannan idan babu matsala ka biya N100, bayan ka gwadashi yayi maka.
Sannan ka latsa SIM Card Changed bayan ka latsa shi, zaka kunna shi domin ya fara aiki, saika shigar da lambar waninka, misali kana iya sa lambar yayanka, ko matarka ko budurwarka, ko mahaifiyarka, lallai lambar da zaka sa ta zama ba taka bace, baka tafiya da ita, manufar wannan shi ne ta wannan lamba za'a sanar da su cewa wayar wane ansace ta, domin ancanza layin da yake kanta, saboda haka ga sabuwar lambar da take kan wayarsa.
Ku kuma ta wannan lamba zaku bi kodai ku kira lambar, ko ku kaiwa yansanda lambar, ko ku rufe wayar, ko kuma akwai sirrin da bakwa bukata wani ya gani, nan take zaku iya goge kanta. Idan kuma manta inda take kayi, ko kuma tana dakin ku amma bata fili saika ziyarci find.nq.com saika latsa Sound nan take zata yi karar sauti, koda bata da chaji zatayi karar da zaka ganta a wuri, amma idan ba batir bazata yi kara ba.
Sannan baya bukatar Username da password, akwai wadanda suke saka "internet" amatsayin username da password wannan airtel baya bukata, idan ya kasance kasa shi, to bazaka yana saurin bude shafi ba, amma zaiyi koda shi, amma ka bar wurinsa ba komai yafi saurin yi.
Kuma shi Airtel yana da tsarin saiti na kai tsaye (Automatic Configuration) kuma shi ba kowacce waya take samun sa'arsa ba, kuma mafi yawa yakan sauka ne da tsohon tsarin zain, wato APN:- internet.ng.zain.com, kuma yakan zo da username da password, wannan baya sauri, sannan yanayin wurin shigar da kowanne seti yana da bam-banci, wato tsari da wurin seta internet a Android Phones, iPhones/iPad, BlackBerry, ko Windows Phones duka da bam-banci, latsa daya daga cikin sunayen wayoyin domin kaga yadda zaka saita taka.
Symbian OS e.g. Nokia N8 Settings>Connectivity>AdminSettings>Mobile Data>Access Point name>
Symbian OS e.g. Nokia C5 Settings>settings>Connection>Packet Data>Access Point>
APN:- internet.ng.airtel.com ...
USERNAME:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
PASSWORD:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
IP/PROXY:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
PORT:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
Sannan kana iya tura kalmar "Settings" zuwa 232 kai tray e zasu turo maka seti daga kamfani, saidai kawai kayi save dinsa, idan sun bukaci lambar sirri "PIN" yayin saukarsa saika sa "1111" ko "0000" ko "1234" ya danganta. Haka idan ka tura basu turo maka saika tura harafin "S" zuwa 232 zasu turo maka insha Allah. Domin karin bayani kayi comment da tambayarka.
Sannan baya bukatar Username da password, akwai wadanda suke saka "internet" amatsayin username da password wannan airtel baya bukata, idan ya kasance kasa shi, to bazaka yana saurin bude shafi ba, amma zaiyi koda shi, amma ka bar wurinsa ba komai yafi saurin yi.
Kuma shi Airtel yana da tsarin saiti na kai tsaye (Automatic Configuration) kuma shi ba kowacce waya take samun sa'arsa ba, kuma mafi yawa yakan sauka ne da tsohon tsarin zain, wato APN:- internet.ng.zain.com, kuma yakan zo da username da password, wannan baya sauri, sannan yanayin wurin shigar da kowanne seti yana da bam-banci, wato tsari da wurin seta internet a Android Phones, Symbian/Java Phones, BlackBerry, ko Windows Phones duka da bam-banci, latsa daya daga cikin sunayen wayoyin domin kaga yadda zaka saita taka.
Ita iPad kala-kala ce, amma wurin setin dinsu kusan daya yake bam-bancin kadana ne, amma ga kadan daga cikinsu, sannan salon duka iPad da iPhone abin daya ne.
iPad 3, iPad 4, iPad Mini Settings>Cellular data>APN settings>APN
iPhones 3G da 4 Settings>General>Network>Mobile Data Network>APN>
iPhone 4S and iPhone 5 Settings>General>Cellular>Cellular Data Network>APN>
APN:- internet.ng.airtel.com ...
USERNAME:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
PASSWORD:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
IP/PROXY:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
PORT:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
Wednesday, 21 March 2018
Sannan baya bukatar Username da password, akwai wadanda suke saka "internet" amatsayin username da password wannan airtel baya bukata, idan ya kasance kasa shi, to bazaka yana saurin bude shafi ba, amma zaiyi koda shi, amma ka bar wurinsa ba komai yafi saurin yi.
Kuma shi Airtel yana da tsarin saiti na kai tsaye (Automatic Configuration) kuma shi ba kowacce waya take samun sa'arsa ba, kuma mafi yawa yakan sauka ne da tsohon tsarin zain, wato APN:- internet.ng.zain.com, kuma yakan zo da username da password, wannan baya sauri, sannan yanayin wurin shigar da kowanne seti yana da bam-banci, wato tsari da wurin seta internet a Android Phones, Symbian/Java Phones, iPhones/iPad, BlackBerry, duka da bam-banci, latsa daya daga cikin sunayen wayoyin domin kaga yadda zaka saita taka.
Domin seta windows phone ta rika browsing wato Windows OS kamar irinsu Nokia Lumia Series, htc series da sauran windows phone saika je Settings>Mobile Networks>Edit APN>
APN:- internet.ng.airtel.com ...
USERNAME:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
PASSWORD:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
IP/PROXY:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
PORT:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
Sannan baya bukatar Username da password, akwai wadanda suke saka "internet" amatsayin username da password wannan airtel baya bukata, idan ya kasance kasa shi, to bazaka yana saurin bude shafi ba, amma zaiyi koda shi, amma ka bar wurinsa ba komai yafi saurin yi.
Kuma shi Airtel yana da tsarin saiti na kai tsaye (Automatic Configuration) kuma shi ba kowacce waya take samun sa'arsa ba, kuma mafi yawa yakan sauka ne da tsohon tsarin zain, wato APN:- internet.ng.zain.com, kuma yakan zo da username da password, wannan baya sauri, sannan yanayin wurin shigar da kowanne seti yana da bam-banci, wato tsari da wurin seta internet a Android Phones, Symbian/Java Phones, iPhones/iPad, ko Windows Phones duka da bam-banci, latsa daya daga cikin sunayen wayoyin domin kaga yadda zaka saita taka.
Domin seta layinka na airtel ya rika browsing akan BlackBerry dinka, ya danganta da kalar BB dinka, tunda ita ma kala-kala ce, sannan kalolinta ya danganta da irin matakin manhajar da take dauke da ( OS version)
Idan kana amfani da OS 7, misali BB Bold 5, saika je Options>Device and Status information>Advanced System settings>TCP/IP> saika latsa APN settings enabled>
Saika shigar da settings da dake kasa.
Idan kuma OS 5 ce dakai misali BB Bold 2 saika latsa Options>Advanced Options>TCP/IP> Saika latsa APN settings enabled> sannan ka latsa APN> ka shigar da settin dinka.
APN:- internet.ng.airtel.com ...
USERNAME:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
PASSWORD:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
IP/PROXY:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
PORT:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
HOMEPAGE:- www.ng.airtel.com ...
Sannan baya bukatar Username da password, akwai wadanda suke saka "internet" amatsayin username da password wannan airtel baya bukata, idan ya kasance kasa shi, to bazaka ga yana saurin bude shafi ba, amma zaiyi koda shi, amma ka bar wurinsa ba komai yafi saurin yi.
Kuma shi Airtel yana da tsarin saiti na kai tsaye (Automatic Configuration) kuma shi ba kowacce waya take samun sa'arsa ba, kuma mafi yawa yakan sauka ne da tsohon tsarin zain, wato APN:- internet.ng.zain.com, kuma yakan zo da username da password, wannan baya sauri, sannan yanayin wurin shigar da kowanne seti yana da bam-banci, wato tsari da wurin seta internet a Symbian/Java Phones, iPhones/iPad, BlackBerry, ko Windows Phones duka da bam-banci, latsa daya daga cikin sunayen wayoyin domin kaga yadda zaka saita taka.
Domin seta android dinka saika bi wadannan matakan
Settings >More Settings>Mobile Network>Access Point Names>saika latsa Menu options> New APN>
ACCOUNT NAME:- Airtel NG ...
APN:- internet.ng.airtel.com ...
USERNAME:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
PASSWORD:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
IP/PROXY:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
PORT:- Karka rubuta komai (Leave it blank)
HOMEPAGE:- www.ng.airtel.com ...
Authentication type:- PAP ...